LABARI DA DUMI-DUMI: An kara shiga Kotu da Sambo Dasuki

LABARI DA DUMI-DUMI: An kara shiga Kotu da Sambo Dasuki

– Yanzu muka samu labarin cewa an kuma gurfanar da Sambo Dasuki a gaban kotu

– Ana zargin tsohon mai ba da shawara kan harkar tsaro da laifuffuka da dama

– Sambo Dasuki yace shi fa bai aikata wadannan laifi ba

LABARI DA DUMI-DUMI: An kara shiga Kotu da Sambo Dasuki

An kara maka Kanal Sambo Dasuki kotu

Yanzu haka NAIJ.com ke samun labari cewa an kara gurfanar da mai ba da shawara kan harkar tsaro a lokacin shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan a gaban kotun tarrayya na Abuja. Tun ba yau ba dai aka kama Sambo Dasuki bisa zargin wasu manyan laifuffuka.

Ana zargin tsohon mai bada shawara a kan harkar tsaro na kasar da laifuffuka har guda 7; daga ciki akwai zargin kama sa da bindigogi da makaman da ba su dace ba. Haka kuma ana zargin Dasuki da satar makudan kudi.

KU KARANTA: An buga tsakanin EFCC da Dame Jonathan a kotu

LABARI DA DUMI-DUMI: An kara shiga Kotu da Sambo Dasuki

Mai ba da shawara kan harkar tsaro a lokacin Jonathan

Gwamnatin Najeriya na karar cewa ta kama Dasuki da makudan kudi sama da Naira Miliyan 40 da kuma wasu daloli a gidan sa da ke Abuja da kuma Sokoto. Shi dai Sambo Dasuki ya bayyanawa Kotu tun tuni cewa yana da gaskiya.

Tsohuwar Uwargidar Najeriya Misis Dame Patience Jonathan tayi nasara a kotu tsakanin a shari’ar da ke tsakanin ta da Hukumar EFCC mai yaki da zamba a kasar dazu a Legas.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sarki Sanusi II yayi kaca-kaca da Shugabannin Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel