Aisha Buhari ta bukaci da a kashe kudi wajen inganta rayuwar mata

Aisha Buhari ta bukaci da a kashe kudi wajen inganta rayuwar mata

-Aisha Buhari ta yi jawabi a hedikwatar majalisar dinkin duniya da kuma ta bukaci a inganta rayuwar mata

- Rayuwar kananan yara mata na cikin hadari

Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari tayi kira ga gwamnatin tarayya data kirkiro wani shiri da zai kula da kananan yara mata da basa makaranta.

Aisha Buhari ta bukaci da a kashe kudi wajen inganta rayuwar mata

Aisha Buhari

Aisha tayi wannan batu ne a ranar Laraba 5 ga watan Afrilu a hedikwatar majalisar dinkin duniya dake birnin New York yayin taron hukumar kidaya ta duniya karo na 50.

KU KARANTA: ‘A kul! Farfesa ka daina haɗa Buhari rigima da majalisa’ – Inji Jam'iyyar APC

Aisha ta samu wakilcin mataimakiyar shugabar kwmaitin kula da mata ta majalisar wakilai Asabe Bashir ne, inda tace yawan kananan mata da basa karatu yayi yawa.

“A yanzu, kananan mata yan shekara 9-10 da basa zuwa makaranta sun kai kashi 1 bisa ukun yawan yan matan dake nahiyar Afirka gaba daya. yaran sun zaman basu da wani buri a rayuwa sakamakon karatunsu ya tsaya saboda rashin kudi da talauci. Wasu kuma auren dole da auren wuri ne sanya su cikin halin nan. musamman ga yan matan da rikicin ta’addanci ya rutsa dasu.” Inji Aisha.

A cewar Aisha Buhari, wannan taron wata hanya ce da kasar Najeriya zata yi kira ga kasashen duniya da su kawo ma kananan mata marasa karatu dauki.

NAIJ.com ta ruwaito Aisha tana fadin: "Abu na farko shine magance matsalar fyade, tare da inganta rayuwar ma’aurata a cikinsu ta hanyar kayyade haihuwa da bada shawarwari, abu na biyu kuwa shine mayar dasu makarantu don su samu ilimin sakandri akalla tare da koyar dasu sana’o’i.”

Uwargida Aisha Buhari ta cigaba da fadin: “Muna kira da kasashen duniya su tallafa ma yan mata, saboda da kudi kadan zamu iya canza musu rayuwa. Da haka ne zamu cimma manufar mu a nahiyar Afirka na muradun karni. Da wannan bayyana ma duniya Najeriya na maraba da duk wani hadin gwiwa da zai kawo cigaba musamman dangane da kananan yara mata.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kungiyar kare hakkin mata sun yi zanga zangar nuna bacin rai da cin zarafin yan mata

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato

Badakalar Maina: Yadda aka raba gidaje 222 da Maina ya kwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel