Matsala: Tsohuwar ministar Jonathan ta shiga ruwan zafi

Matsala: Tsohuwar ministar Jonathan ta shiga ruwan zafi

- Wata kotun Najeriya ta tuhumi tsohuwar ministar albarkatun man fetur Diezani Alison-Maudeke da wasu jami'an hukumar zaben kasar

- Hukumar INEC da laifin yin amfani da kudi da zummar murde zaben shekarar 2015

Tsohuwar ministar Jonathan

Tsohuwar ministar Jonathan

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati ce dai ta gurfanar da jami'an INEC uku a gaban kotun tarayya da ke Lagos karkashin mai shari'a M. B. Idris, inda ta zarge su da karbar cin hanci N265m daga wurin Ms Alison-Madueke domin sauya sakamakon zaben 2015.

NAIJ.com ta samu labarin cewa jami'an INEC din da ake tuhuma su ne Christian Nwosu, Yisa Olanrewaju Adedoyin da Tijani Bashir.

KU KARANTA: Annobar sankarau ta bulla a Arewa

Da yake jawabi a gaban kotun, Christian Nwosu ya amince da karbar cin hancin N30m daga tsohuwar ministar albarkatun man fetur din da zummar yin magudin zaben.

Diezani Alison-Maudeke ba ta kotu a lokacin da aka ayyana ta a cikin wadanda ake tuhuma da lafin halasta kudin haramun.

Tsohuwar ministar dai ba ta yi raddi kan wannan tuhuma ba, sai dai a baya ta sha musanta zarge-zargen da ake yi mata na cin hanci da rashawa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai wani tsohon ma'aikacin Jonathan dinne ya ke bada ba'asi a kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel