Sankarau: Anyi ma mutane 1,400 alurar rigakafi a Bauchi

Sankarau: Anyi ma mutane 1,400 alurar rigakafi a Bauchi

Ma'aikatan kiwon lafiya a Najeriya sun fara rigakafin cutar sankarau a wani yunkurin na dakatar da ci gaba da yaduwar cutar.

Sankarau: Anyi ma mutane 1,400 alurar rigakafi a Bauchi

Anyi ma mutane 1,400 alurar rigakafi na cutar Sankarau a Bauchi

Kamfanin dilancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa a ranar Alhamis, 6 ga watan Afrilu, sashin ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Bauchi tayi alurar rigakafi ga mutane 1,400 da kuma ma’aikatan gidan yari 240 a kan annobar sankarau wato Cerebro Spinal Meningitis (CSM).

KU KARANTA KUMA: Ministan Buhari na cikin babbar matsala

Mista Adamu Gamawa, shugaban hukumar, ya bayyana hakan a Bauchi a ranar Alhamis lokacin wata hira da kamfanin dilancin labaran Najeriya (NAN).

A cewar sa, an dauki wannan mataki ne domin hana yaduwar cutar a tsakanin fursunoni saboda cunkoson gidan yari.

Ya kuma bayyana cewa za’a dauki matakai makamancin wannan a guraren jama’a don hana yaduwar annobar.

Shugaban ya bayyana cewa hukumar ta bukaci Karin alurar rigakafi daga hukumomin lafiya don daukar mataki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya kamata mutun ya garzaya asibiti da zaran ya tsinci kansa a wannan yanayi don gwajin cutar kanjamau:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel