Sanatoci sun nuna bacin ransu da Saraki akan ganawarshi da shugaban kasa

Sanatoci sun nuna bacin ransu da Saraki akan ganawarshi da shugaban kasa

- Sanatoci na fushi da Shugaban majalisan dattawa,Bukola Saraki, saboda rashin tattauna ainihin abinda ya tayar da kura tsakanin su da fadar Shugaban kasa

- Yan majalisan sun nuna bacin ransu akan rashin maganan da Saraki yayi akan rashin cire Magu bayan sunki tabbatar da shi sau biyu

- Sanatoci sun ce shin meyasa Saraki bai fadawa Buhari abinda Farfesa Iste Sagay yayi

Sanatoci na fushi da Saraki akan ganawarshi da Buhari

Sanatoci na fushi da Saraki akan ganawarshi da Buhari

Sanatocin majalisan dattawa sun nuna bacin ransu akan rashin maganan da Saraki yayi lokacin ganawarshi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranan Litinin, 3 ga watan Afrilu.

NAIJ.com ta ruwaito cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara, domin sasanta rikicin da ke tsakanin bangarorin guda 2.

KU KARANTA: Wani ministan Buhari ya shiga matsala

Amma da dukkan alamu, wannan wuta bata mutu ba har yanzu yayinda sanatoci suka nuna bacin ransu akan rashin tattauna abinda ya tayar da kuran.

Yan majalisar dattawan sun shiga ganawa misalin karfe 11 na af a ranan Talata, inda suka tattauna abubuwa daban-daban.

A ganawar, Saraki ya fadawa majalisa cewa abinda ya tattauna da shugaba Buhari shine zancen kasafin kudin 2017 da kuma tabbatar da ministoci guda biyu.

Wata majiya a majalisan dattawa tace lokacin da Saraki ya bayyana musu abinda suka tattauna da shugaba Buhari cewa a kashe wutan. Kawai sai fuskokin wasu sanatoci ya fara murtukewa akan rashin maganarsa akan cire Magu, Hameed Ali da kuma zagin da Farfesa Itse Sagay yake masa.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel