Tofa! Annobar cutar Sankarau ta bulla a wata sabuwar jiha a Arewa

Tofa! Annobar cutar Sankarau ta bulla a wata sabuwar jiha a Arewa

Rahotanni daga jahar Adamawa a arewacin Najeriya na cewa an samu barkewar cutar sankarau a wasu sassan jahar wannan cutar ana daukar ta ne ta iska, a kwayar halittar da ba a gani da ido, kuma takan shafi abinda keda da alaka da numfashi.

Annobar cutar Sankarau

Annobar cutar Sankarau

Bayanan na cewa mutane na kara kamuwa da cutar ne sakamakon matsalar zafi da ake fama da ita, a wannan lokaci koda yake hukumomin jahar na cewa lamarin bai kai matsayin annoba ba, kuma sun ce suna daukar matakin gaggawa a duk inda aka samu bayanan bullar cutar.

NAIJ.com ta samu labarin cewa da yake tabbatar da bullar cutar Dr Raymon Dauda, wani likita kuma shugaban asibitin Vanada Hospital, wanda ke zaman kansa a Yola, yace ya zuwa yanzu sun yi jinyar wasu da suka kamu da cutar.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara yace sabon Allah ne ya kawo cutar Sankarau

Ko wadanne matakai ya kamata jama’a su dauka don yin rigakafin kamuwa da cutar?, masanin kiwon lafiya Dr Raymon Dauda, ya bayyana cewa mafi yawancin alkalumman gwamnati na bayyana yawan wadanda suka mutu a asibiti a yayin da wasu ke mutuwa a gidajensu saboda rashin abin hannu da za su dauki dawainiyar kansu a asibiti.

To sai dai kuma, yanzu haka hukumomin lafiya na daukar matakai na shawo kan matsalar ta hanyar riga kafi da ba da magani da kuma yekuwar wayar da kai a kan kaucewa kwanciya a cikin dakuna saboda tsananin zafi. Dr Fatima Atiku Abubakar, itace kwamishiniyar kiwon lafiya a jihar Adamawa, ta bayyana matakan da suka dauka.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Yan Najeriya na tsokaci game da kasafin kudin fannin lafiya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel