Jami'an tsaro ne ke kara rura wutar rikicin kudancin Kaduna - Elrufa'i

Jami'an tsaro ne ke kara rura wutar rikicin kudancin Kaduna - Elrufa'i

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce zata kwashe jami’an tsaron dake kudancin jihar Kaduna domin ta gano cewa mafi yawancinsu ‘yan yankinne, lamarin da yasa take zargin suna cikin dalilian da suka sa harkokin tsaro suka tabarbare a yankin.

Gwamnan Kaduna El-rufa'i

Gwamnan Kaduna El-rufa'i

NAIJ.com ta samu labarin cewa da yake jawabi a wurin wani taron manyan malaman addinin Kirista da na Musulmi a jihar Kaduna, gwamna Nasir Ahmed El-Rufa’i ya ce gwamnatinsa zata bi-biyi tashe tashen hankulan da aka samu har guda Goma sha Biyar, da kuma tabbatar da hukunta duk wadanda aka samu da hannu a ciki.

Wasu daga cikin manyan malaman addinan da suka halarci wannan taro sun jingina matsalar tsaron a kan rashin gudanar da irin wannan taro na manyan malaman addinan da zasu taimaka wajan samar da zaman lafiya da tsaro a jihar Kaduna.

KU KARANTA: Yakin basasa na neman barkewa a majalisa

Sai dai kuma limamin masallacin juma’a na Al-Munnar, Sheik Tukur Al’munnar, ya zo da mabanbancin ra’ayi, inda ya bayyana cewa duk maganar zaman lafiyar da za’a yi bata kai wadda ke cikin littattafan addinan biyu ba, dan haka a nasa ra’ayi, malaman addinan ne ya kamata su gayyaci gwamnati domin bata shawara a maimakon ita ta gayyace su.

Malamin ya kara da cewa idan aka wayi gari malaman addinan biyu suka bada tabbacin zaman lafiya a jihar Kaduna, babu shakka haka zata cimma ruwa domin alhakin ya rataya ne a kawunansu.

Wannan shine karo na farko da gwamnatin El-Rufa’i, cikin kusan shekaru biyu ta tattara manyan malaman addinin Kirista da na musulmi domin tattaunawa akan matsalolin tsaro da suka addabi jihar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai ku kalli yadda yaki ya dai daita yara a kudancin Kaduna din

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel