An kwantar da wani ɗan majalisa bayan yaci na jaki a hannun jama’an mazaɓarsa

An kwantar da wani ɗan majalisa bayan yaci na jaki a hannun jama’an mazaɓarsa

Wani daa majalisar dokoki dake wakiltan mazabar Bosso, Paiko na jihar Neja Salihu Adamu na can kwance a Asibiti bayan ya sha da kyar a hannun al’ummar dayake wakilta lokacin da suka yi masa dukan tsiya.

An kwantar da wani ɗan majalisa bayan yaci na jaki a hannun jama’an mazaɓarsa

Dan majalisa Salihu Adamu

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin 3 ga watan Afrilu lokacin da dan majalisar ya kai ziyara wani kauye don halartan taron siyasa, NAIJ.com ta tattaro bayanai dake nuna a wurin taron ne aka samu wasu matasa da suka far masa da duka, har ma suka farfasa masa mota.

KU KARANTA:Gobara ta tashi a filin sauka da tashin jirage na Aminu Kano

Da kyar da sudin goshin yansanda suka kwace shi bayan matasan sun mai lilies, har ya fita hayyacinsa.

NAIJ.com ta gano cewar tun da dadewa ne matasan yankin ke jin haushin dan majalisar sakamakon dauke kafa daga yankinsu da rashin kawo musu ziyara tun bayan da suka zabe shi, kimanin shekaru 2 kenan.

Rahotanni sun bayyana cewar da isan dan majalisar inda za’a yi taron, sai matasan suka bukaci daya bar wajen taron, amma dan majalisar yayi biris dasu, ko a jikinsa.

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace “daya daga cikin matasan ne ya fara sharara masa mari, daga nan sai wani kuma ya naushe shi a ciki, hakan yasa ya fadi tim! a kasa.

“Faduwarsa ke da wuya, kawai sai sauran matasan suka dinga cusa masa hannu.” Inji majiyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kana goyon bayan a rushe majalisar dattawa? Saurari ra'ayin jama'a a nan:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel