Tinubu ya musanta zargin haddasa rikici a majalisar dattawa

Tinubu ya musanta zargin haddasa rikici a majalisar dattawa

Jagoran jam’iyyar APC Ahmed Bola Tinubu yace wasu mutanen kawai ne ke amfani da sunansa wajen rura rikici a majalisar dattawa.

Tinubu ya musanta zargin haddasa rikici a majalisar dattawa

Jagoran APC Tinubu

Tinubu ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa data samu sa hannun hadiminsa Tunde Rahman, inda ya karyata wani rahoto dake cewa wai yana tunzura EFCC dasu kama sanatocin jam’iyyar PDP, Rahman yace Tinubu yafi karfin yin haka, inda yace Tinubu na girmama majalisar dattawa, don haka ba zai ci mutuncin tab a ko yayi mata zagon kasa.

KU KARANTA: Gobara ta tashi a filin sauka da tashin jirage na Aminu Kano

“Duk da cewa an san ba lallai mu hada ra’ayi da PDP ba, amma a matsayin Tinubu na tsohon sanata, yana girmama majalisar dattawa, kuma ba zai wani abu da zai ci mutuncinta ba. Saboda ba haka yake siyasar ba, fahimtar sa da na yan PDP ta bambamta, saboda shi siyasar sat a ilimi ce.

“Tinubu zai baiwa PDP kashi a duk inda suka hadu a zabe, amma yafi karfin ya dinga zaginsu ko cin mutuncinsu ta hanyar watsa jita jita ko karairayi, ba haka yake ba, don haka babu kamshin gaskiya cikin batun da ake yadawa. Wasu ne kawai ke amfani da sunan Tinubu don bata Magu.”

Daga karshe Rahman yace “Wasu ne masu bukata ta kashin kai suka shirya wannan rahoto, kuma anyi walkiya mun gansu, su sani yaki da cin hanci da rashawa yanzu aka fara, da haka ne zamu ceto kasar mu.” Kamar yadda NAIJ.com ta samu rahoto.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wai ko dai ma ayi watsa da majalisar dattawa ne? kalli ra'ayin jama'a anan;

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel