Hukumar EFCC ta yi caraf da tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu

Hukumar EFCC ta yi caraf da tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu

Hukumar yaki da almundahana da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta cika hannu da tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu kan zarginsa da take yi da bindiga da sama da naira biliyan 3.6 inji rahoton jaridar Vanguard.

Hukumar EFCC ta yi caraf da tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu

Babangida Aliyu

Su dai wadannan makudan kudade kudade ne da aka samu daga ribar siyar da kaso 16 cikin 26 na hannun jarin gwamnatin jihar Neja dake cikin kamfanin lantarki na North-South Power Ltd, har way au EFCC na tuhumar Babangidan da wakaci-waka tashi da wasu zamnbar kudi naira biliyan 2 da gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan ta baiwa jihohi don kare gurbacewar yanayi a shekarar 2015.

KU KARANTA: Jami'an kwastam sun kama motocin sumogan shinkafa guda 7, 3 sun jikkata

Majiyar Vanguarda ta shaida mata cewar tun a ranar Talata 4 ga watan Afrilu ne hukumar EFCC ke tsare da tsohon gwamnan, inda ya amsa gayyatan hukumar da misalin karfe 10 na safe, majiyar ta bayyana cewar Babangida yana shan tambayoyi ne daga wasu kwararrun matambaya daga cikin jami’an hukumar.

EFCC na tuhumar tsohon gwamnan da zargin karya alfarmar ofishinsa da kuma satar kudade, da alamu kuma zara gurfanar da shi gaban kotu, muddin dai bincikenta ya nuna mata yana da hannu cikin badakalolin da take zarginta dasu akai.

Majiyar ta cigaba da bayyana cewar EFCC ta dage kan lallai sai Aliyu yayi mata bayani kan yadda ya kashe naira biliyan 2 kudin kare gurbatan yanayi da jihar Neja ta samu daga gwamnatin tarayya, bugu da kari EFCC na bincikar wasu kamfanuwa guda uku da ke da hannu cikin badakalar, wadanda suka hada da; I D Sabon, MJ Eco da Secta Plus.

Ana zargin kamfanin ID Sabon mallakin tsohon sakataren gwamnatin jihar ne, Saidu Nddako Idris, wanda ta samu kwangilar naira miliyan 847, inda kuma aka biya ta naira milyan 800 ta hannun shugaban ma’aikatan gidna gwamnati Umar nasko, wanda shi kuma ya mika kudaden zuwa ga tsohon gwamnan.

Kamfanin MJ Eco kuwa mallakin wani abokin Ibrahim Nasko ne, wato kanin Umar Nasko, Nuhsinuazali Jibril wanda aka biya shi kudi nara miliyan 487 don gudanar da wani aikin da har yanzu ba’a ga aikin ba. Suma wadannan kudade an canza su zuwa dalar Amurka ne, inda aka mika su ga Umar Nasko, shima ya mika u ga tsohon gwamnan.

NAIJ.com ta tattaro bayanan da suke nuna cewa duba da binciken da EFCC ke gudanarwa, kamfanin Secta Plus ne kadai ta gudanar da kwangilar da aka bata. Don haka “Sai mun kammala bincike kafin mu sake shi, don kuwa akwai sauran tambayoyi, kuma yana bamu hadin kai” inji wani jami’in hukumar daya shaida ma Vanguard a daren jiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga yadda EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban NNPC Andrew Yakubu gaban kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel