CBN ta fitar da lamba ta musamman da za a kira domin korafe korafe akan rashin samun kudaden canji

CBN ta fitar da lamba ta musamman da za a kira domin korafe korafe akan rashin samun kudaden canji

Babban bankin Najeriya CBN ya fitar da lambar waya da adireshin Imel na musamman da mutane za su iya kira idan aka hana su kudaden canji a bankuna a fadin kasar nan.

CBN ta fitar da lamba ta musamman da za a kira domin korafe korafe akan rashin samun kudaden canji

CBN ta fitar da lamba ta musamman da za a kira domin korafe korafe akan rashin samun kudaden canji

Banki ya ce duk wanda aka ki canja masa alawus na fita kasashen waje a cikin awanni 24, ko kuma kudaden kula da lafiya ko kuma kudaden makaranta a cikin awanni 48 toh ya na da hurumin ya kira ya shigar da kara ta wannan lambar ko kuma ya tura sako zuwa adireshin Imel din.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Jihar Kaduna ta rusa gidan Inuwa AbdulKadir

An bukaci masu shigar da korafin da su bayyana sunan bankin da kuma ofishin da suka samu matsalar.

Haka kuma bankin ya roki mutane da cewar kada su sake su sayi dala akan farashin fiye da N360.

Ya kuma musanta jita jitan cewar bankunan ba sa siyar da dalar ne saboda ba su da isassun dala, bankin ya ce a kullum dala miliyan 80 yake fitarwa domin rabawa bankuna a fadin kasar nan.

Ga Lambar: 07002255226, da kuma adireshinn imel din: cpd@cbn.gov.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin kana danasanin zaban shugaba Buhari? kalli wannan bidiyon:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel