Shugaba Buhari ya bada umurnin gina hanyoyi 36 a Najeriya - Inji Sanata Gaya

Shugaba Buhari ya bada umurnin gina hanyoyi 36 a Najeriya - Inji Sanata Gaya

- Gwamnatin tarraiyya ta bada umurnin a cigaba da amfani da kasafin kudin shekara 2016 har zuwa watan Mayu bana saboda a samu cikakkiyar shekara guda ana amfani da kasafin ganin

- Shugaban kwamitin kula da kasafin kudi a majalisar dattawa, sanata Danjuma Goje ya bayyana cewa an aiwatar da kusan rabin kasafin kudin na 2016

Gwamnatin tarraiyya ta bada umurnin a cigaba da amfani da kasafin kudin shekara 2016 har zuwa watan Mayun 2017 saboda a iya samu cikakkiyar shekara guda ana amfani da kasafin ganin cewa ranan 6 ga Watan Mayu 2016 ne Shugaba Buhari ya sa hannu ta zama doka.

Ministan kudi Madam Kemi Adeosun ce ta bayyana haka a wata takarda da ta aika wa hukumomin gwamnati.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya gabatar da kasafin kudi wanda aka yiwa lakabi da kasafin kudin gina kasa a gaban hadaddiyar majalisa a watan Disambar shekarar 2015.

NAIJ.COM ta tattaro cewa har zuwa yanzu dai alkaluma na nuna cewar an aiwatar da kusan rabin kasafin kudin na 2016 kamar yadda sanata Danjuma Goje, shugaban kwamitin kula da kasafin kudi a majalisar dattawa ya bayyana.

KU KARANTA: Za mu yi wa Abdulmumini Jibrin Kiranye da ga majalisa saboda rashin kunyar da ya yi wa Buhari

Rashin kyawon hanyoyi dake zama hujjar yajin aikin wasu ma’aikatan gwamnati kamar na ma’aikatar man fetur, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin a yi su a kasafin kudin, kamar yadda shugaban kwamitin kula da hanyoyi sanata Kabiru Gaya, ya yi karin bayanin cewa ana gab da fara gyare gyaren hanyoyi 36 da shugaban kasa ya umurci a gyara a fadin kasar.

Sanata Yusuf Abubakar, daya daga cikin ‘ya’yan kwamitin kula da harkokin kudi a majalisar dattawa ya bayyana cewa kawo yanzu suna kan tattaunawa da sauran takwarorinsu domin tabbatar da kaucewa kura-kurai makamantan na bara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon zargin takardar shaidar na sanata Dino Melaye

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel