Ka ji shirin da Gwamnonin Najeriya ke yi?

Ka ji shirin da Gwamnonin Najeriya ke yi?

– Muna samun abin da Gwamnoni ke shirin yi a halin yanzu

– Muna da labarin cewa Gwamnonin Jihohin Najeriya na nema su karbo wani makukun bashi

– Za a nemo bashin ne daga wata kasa domin raya harkar noma a kasar

Ka ji shirin da Gwamnonin Najeriya ke yi?

Gwamnoni Jihohi na shirin karbo bashi

NAIJ.com na da labari cewa Gwamnonin kasar nan na shirin ciwo bashi daga kasar China domin habaka harkar gona a Jihohin da ma Birnin-Tarayya. Yanzu haka dai shugaban kasa Buhari ya nemi Gwamnonin su zauna da Ministoci.

Ministan noma na kasar Audu Ogbeh da kuma Gwamna Abdulaziz Yari wanda shi ne shugaban Gwamnoni su ka bayyana haka kwanan nan a Abuja. Za ayi amfani da wannan makudan kudi domin sayo kayan noma irin su tarakata da kayan feshi da sauran su.

KU KARANTA: An ga Gwamna Ganduje da Shekarau suna tattaunawa

Ka ji shirin da Gwamnonin Najeriya ke yi?

Shugaba Buhari tare Gwamnonin Najeriya a taro

Bashin dai ya kai Dala Biliyan 4.5 wanda ba karamin kudi ba ne. Za a karbo aron kudin ne daga kasar Sin watau China sannan kuma a iya biya nan da shekaru 20 masu zuwa. Shugaba Buhari ya nemi Gwamnonin su zauna da Ministar kudi da kuma na kasafi kasar domin samun matsaya.

Mai girma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi yayi kira ga masu rike da shugabanci da su kara zage dantse domin cigaban yankin da ma Najeriya gaba daya. Yace wasu wasu Gwamnonin ba su da aikin yi sai zuwa Kasar China domin su karbo bashi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan Najeriya duk barayi ne wai?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel