Za mu yi wa Abdulmumini Jibrin Kiranye da ga majalisa saboda rashin kunyar da ya yi wa Buhari

Za mu yi wa Abdulmumini Jibrin Kiranye da ga majalisa saboda rashin kunyar da ya yi wa Buhari

Jama’ar mazabar Kiru da Bebeji sun ce a shirye suke suyi wa dan Majalisar su Abdulmumini Jibrin Kiranye saboda maganganun da yayi akan Buhari na batanci.

Za mu yi wa Abdulmumini Jibrin Kiranye da ga majalisa saboda rashin kunyar da ya yi wa Buhari

Jama’ar mazabar Kiru da Bebeji sun ce a shirye suke suyi wa dan Majalisar su Abdulmumini Jibrin Kiranye

Jama’ar yankin mazabun da yake wakilta sun dunguma ne zuwa ofishin jam’iyyar APC da ke jihar Kano domin mika wasikar su na neman yi masa Kiranye.

KU KARANTA KUMA: Babban malamin musulunci Sheikh Alhassan Saeed ya rasuBabban malamin musulunci Sheikh Alhassan Saeed ya rasu

Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Kiru yace babu wanda zai hana su yi wa Abdulmumini kiranye akan irin maganganun da ya yi wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Da yake mika wasikar ga shugaban jam’iyyar na jihar Kano jogoran tafiyar yace “Da farko dai in so in sanar muku cewa ba ma tare da Abdulmumini Jibrin akan zantuttukan da yayi kan rashin lafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.”

NAIJ.com ta samu labarin cewa Sarkin yakin Jibrin Abdulmumini shi ma ya nuna rashin jin dadin sa akan furucin da yayi sannan yace a gaskiya fa basa tare dashi.

“Jibrin ya nu cewa shi ma barawo domin da kansa ya tona yadda suke satan kudin talakawa a tsawon shekarun da yayi yana majalisar wakilai.

“Babu wani abin da yayi wa mazabun sa na azo a gani a tsawon shekarun da yayi a majalisa."

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Jihar Kaduna ta rusa gidan Inuwa AbdulKadir

Daga karshe sun ce za su yi kungiya domin zuwa Abuja su roki shugaban kasa akan furucin da Jibrin yayi dangane da rashin lafiyar sa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon wata yar Arewa da ke gargadin yan Arewa kan shugaba Muhammadu Buhari:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar Peace Corps ta bukaci babbar kotun tarayya ta gaggauta gabatar da shugaban 'yan sanda gidan kaso

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel