Kotu a Abuja ta hana a binciki Ribadu, Farida, Lamorde da Magu

Kotu a Abuja ta hana a binciki Ribadu, Farida, Lamorde da Magu

Babbar kotun tarayya da ke Jabi, Abuja, ta hana wani roko da aka shigar a kotun cewa ta umarci babban Atoni Janar na Tarayya ya binciki tsoffin shugabannin hukumar hana al’mundahana da zambar kudade, wato EFCC.

Kotu a Abuja ta hana a binciki Ribadu, Farida, Lamorde da Magu

Kotu a Abuja ta hana a binciki Ribadu, Farida, Lamorde da Magu

Mai shari’a Abba-Bello Muhammed ne ya yi watsi da wannan batu na hana binciken, bayan ya saurari korafin da lauya Frank Tietie ya shigar. Mai shari’a ya soke korafin ne da ke cikin waka kara mai lamba M/4853/17 Da George Ubor ya shigar.

KU KARANTA KUMA: Rahama Sadau ta ƙaro wulaƙanci: Kalli wasu kyawawan Hotunan ta

Ya ce babu wani dalili ko hujja da mai shigar da kara ya gabatar da zai sa mai shari’ar ya tilasta a binciki Nuhu Ribadu, Farida Waziri, Ibrahim Lamorde da kuma Ibarahim Magu.

NAIJ.com ta ruwaito inda, Alkalin ya kara da cewa mai karar ba shi da wata hujja kuma ba shi iko a karkashin kowace doka da har zai nemi kotun ta tilasta wa Atoni Janar ya binciki tsoffin shugabannin EFCC din, ko kuma ta ce masa ga wadanda zai bincika.

“Na yi nazarin dukkan takardun korafin ku, amma hakan ba zai yiwu ba, har sai idan ku na da kwakwkwarar madogara daga dokar kasa, kafin a saurari wannan korafi na ku.”

KU KARANTA KUMA: Daga karshe: Majalisa ta maido wadanda ta kora

Ya kara da cewa lauya mai zaman kan sa ba shi da hurumin da zai sa kotu ta tilasta wa Atoni Janar ya binciki shugabannin EFCC.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wasu yan Najeriya da sukayi sharhi bayan dawowar shugaban kasa daga dogon hutu da yayi a birnin Landan.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel