Idan da zunubi na sa a kamu da cutar Sankarau da kusan duka ‘yan siyasa sun kamu – Inji Sanata

Idan da zunubi na sa a kamu da cutar Sankarau da kusan duka ‘yan siyasa sun kamu – Inji Sanata

Sanata mai wakiltan jihar Bayelsa Ben Bruce ya zolayi gwamnan jihar Zamfara kan cewa da yayi wai aikata zunubai ne da mutane su keyi ya sa ake ta fama da cutar Sankarau a wasu sassan kasar nan.

Idan da zunubi na sa a kamu da cutar Sankarau da kusan duka ‘yan siyasa sun kamu – Inji Sanata

Sanata Ben Bruce ya kalubalanci Abdulaziz Yari

Sanatan yace bai yarda da abinda gwamna AbdulAziz Yari yace ba wai “aikata laifi ne da mutane sukeyi ke kawo cutar Sankarau.”

KU KARANTA KUMA: Daga karshe: Majalisa ta maido wadanda ta kora

“ A na kama cutar Sankarau ta dalilin yaduwar kwayar cuta ne ba don an aika ta laifi ba.

“Idan zunubi ne ke kawo cutar Sankarau da dukkan mu ‘yan siyasa mun kamu da cutar."

A bangare daya, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi ba’a ga gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, kan cewa da yayi Allah na hukunta yan Najeriya ne da cutar sankarau da ya kashe akalla mutane 336 a Najeriya.

Sarki Sanusi yace: “ Wannan magana da kayi bai yi daidai da Karantarwan Addinin Musulunci ba.

“Idan baka da maganin rigakafi ka ce baka da shi, sai kaje ka nemo wa mutanen jihar ka kawai.”

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon rikicin Hausawa da Yarbawa a garin Ile Ife.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel