Nayi tsufa da zama gwamna – El-Rufai

Nayi tsufa da zama gwamna – El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya kaddamar da cewa yayi tsufa sosai da zama gwamna

- Ya mayar da hankali ga cewa kwararrun matasa ne ya kamata su dunga shugabantar jihohin Najeriya

- Ya ce yaso ace ya zamo gwamna ne lokacin da yake da shekara 40

Nayi tsufa da zama gwamna – El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufai yace yayi tsufa sosai da zama gwamna

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana kansa a matsayin mutumin da ya tsufa da zama gwamna.

KU KARANTA KUMA: Rahama Sadau ta ƙaro wulaƙanci: Kalli wasu kyawawan Hotunan ta

Da yake magana a Kaduna kan bukatar sake fasalin ma’aikatar jihar, El-Rufai ya mayar da hankali kan cewa akwai bukatar matasa da yan Najeriya masu gwaninta su shugabanci jihohi a kasar.

Gwamnan ya nace kan cewa ba wa matasa damar shugabantar kasar shine hanya mafi dacewa.

“Aikin gwamnati na matasa ne. nayi tsufa da zama gwamna. Ya kamata ace na zamo gwamna lokacin da nake shekaru 40.

“Wannan shekarun ne ya kamata saboda lokacin mutun na da kuzari, mutun na da gwanancewa, mutun na iya daukar dogon sa’oi. Na san yawan sa’oin da nake dauka lokacin na nake a matsayin ministan birnin tarayya, bazan iya yi haka ba a yanzu.

“Ya kamata muba matasa hanya sannan kuma a Kaduna, muna aiki a kan haka.”

KU KARANTA KUMA: Daga karshe: Majalisa ta maido wadanda ta kora

Tsohon Ministan babban birnin tarayyan, ya bayyana cewa gwamnatin sa na duba ga sake faslin al’amuran gwamnatin jihar don inganta jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin kana danasanin zaban shugaba Buhari? kalli wannan bidiyon:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel