An yi kira ga Gwamnoni su tashi tsaye

An yi kira ga Gwamnoni su tashi tsaye

Mai girma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi yayi kira ga masu rike da shugabanci da su kara zage dantse domin cigaban yankin da ma Najeriya gaba daya

An yi kira ga Gwamnoni su tashi tsaye

Wani taro da Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya soki irin tsarin tafiyar wasu shugabannin Arewa yace sam akwai gyara. Mai marataban yayi wannan magana ne wajen wani taro da Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya domin kiran masu hannun jari.

Sarkin yace wasu Gwamnonin ba su da aikin yi sai zuwa Kasar China domin su karbo bashi. Mai martaban yace akwai gyara a lamarin kasar. Tun kafin Sarkin ya fara jawabi dai ya nemi a yafe masa don yace ya san wasu sai sun ji haushin maganganun sa.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya gargadi Gwamnonin Arewa

An yi kira ga Gwamnoni su tashi tsaye

Mai martaba Sarkin Kano Sanusi II

Sarkin yayi kira da shugabanni su cigaba da ayyukan kirki da magabatan su suka faro domin cigaban kasar. Kamar dai yadda kuma NAIJ.com ta kawo maku labari Sarkin yayi kaca-kaca da kalaman da Gwamnan Zamfara ya furta a jiya na cewa Ubangiji ne ya kawo sankarau.

A wannan taro da Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya Sarkin Musulmi mai martaba Alhaji Sa’adu Abubakar III yayi magana shi ma inda ya gargadi Gwamnonin Najeriya da su yi aiki ko su ga ba yadda su ka so a zabe mai zuwa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicin yakin Basasa na Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel