Sojojin Najeriya sun taka rawar gani

Sojojin Najeriya sun taka rawar gani

Sojojin Najeriya sun karbo shanu da dama daga hannun barayi a Garin Bauchi kamar yadda muke samun labari daga hukumar dillacin labarai na kasa NAN

Sojojin Najeriya sun taka rawar gani

Madalla: Sojojin Najeriya sun taka rawar gani a Bauchi

Rundunar Sojojin Najeriya sun yi nasarar karbo shanu da tumaki da a Garin Ningin Jihar Bauchi. NAIJ.com ta samu labarin cewa Sojojin sun karbe shanu 39 da kuma awaki kusan 50 a Kauyen Dangarfa da ke Jihar ta Bauchi.

Manjo Joseph Afolasade wanda shi ne Mataimakin Darektan yada labarai na Rundunar Sojin ya bayyana haka a farkon makon nan. Manjo Afolsade ya bayyana cewa Laftana Haruna Hassan ne ya jagoranci tawagar Sojojin.

KU KARANTA: Malaman Jami'a za su shiga yajin aiki

Sojojin Najeriya sun taka rawar gani

Sojojin Najeriya sun gano dabbobin da aka sace

Bayan Sojojin sun gano barayin shanun ne su ka bi su cikin daji nan fa barayin su ka ci na kare su ka tsere su ka bar dabbobin a nan. Wannan dai abin a jinjinawa Sojojin ne ganin yadda barayin dabbobi su ka addabi Jama’a.

Mai girma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II yayi kira ga masu rike da shugabanci musamman a Arewa da su kara zage dantse domin cigaban yankin da ma Najeriya gaba daya yace ba shakka an bar Arewa a baya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicin Ile Ife na Kasar Yarbawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel