‘Najeriya zata dinga samar da kayayyakin amfaninta a ƙarƙashin jagoranci na’ – Shugaba Buhari

‘Najeriya zata dinga samar da kayayyakin amfaninta a ƙarƙashin jagoranci na’ – Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da tsarin farfado da komadar tattalin arzikin kasar nan a ranar Larab 5 ga watan Maris a fadar gwamnati, dake Abuja.

‘Najeriya zata dinga samar da kayayyakin amfaninta a ƙarƙashin jagoranci na’ – Shugaba Buhari

Shugaba Buhari yayin kaddamar da tsarin

Ma’aikatan kasafin kudi da tsare tsare ne ta kirkiro wannan tsarin farfado da tattalin arzikin kasar, kuma ya kunshi manufofi guda 60 da ake sa ran zasu fitar da kasar nan daga halin matsin tattalin arziki, tare da daura kasar akan turbar samu cigaba mai daurewa.

KU KARANTA: A yau da misalin karfe 11 Buhari zai ƙaddamar da shirin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa

‘Najeriya zata dinga samar da kayayyakin amfaninta a ƙarƙashin jagoranci na’ – Shugaba Buhari

Shugaba Buhari tare da Dogara, Yari

Wasu daga cikin manufofin tsarin shine daidaita yanayin kasuwanci, inganta harkar mai da habbaka kasuwanci kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

Dayake jawabi, mai gayya mai aiki, shugaban kasa Muhamamdu Buhari yace gwamnatinsa a shirye take ta mayar da Najeriya kasar dake samar da yawancin bukatunta ta hanyar samar da su a nan gida ba tare da an shigo dasu daga kasashen waje ba.

“Zamu sauya kasar akalar tattalin arzikin kasar daga cima zaune zuwa mai samar da yawancin ababen da take bukata.” Inji Buhari

Shima ministan kasafin kudi da tsare tsare Sanata Udo Udoma yayin da yake jawabin maraba, yace wannan tsarin yayi daidai da manufar sauyi da gwamnatin Buhari ta dauru akai. “Don haka wannan turba ce mikakkiya da zata farfadon da tattalin arzikin kasa.” Inji shi

Cikin wadanda suka samu halartan taron akwai shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, Kaakakin majalisa Yakubu Dogara, shugaban kungiyar gwamnoni Abdul Aziz Yari, dukkaninsu sun yaba da tsarin tare da jaddada goyon bayansu ga shirin na gwamnatin tarayya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin ka san farashin kayayyakin masarufi a kasuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel