Anshirya tsaf don sake bude sansanin yan bautar kasa na jihar Borno

Anshirya tsaf don sake bude sansanin yan bautar kasa na jihar Borno

Hukumar Kula da masu bautar kasa, NYSC ta sanar da cewa ta na aiki sosai domin ganin an sake bude sansanin masu bautar kasa a Maiduguri, ganin cewa a yanzu an samu dawowar zaman lafiya a jihar.

sansanin yan bautar kasa

sansanin yan bautar kasa

Darekta Janar na NYSC, Sulaiman Kazaure ne ya fadi haka ranar Talata yayin da ya ke zantawa da ’yan jarida a Maiduguri.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Kazaure ya kara da cewa hukumar ta kagara matuka wajen ganin ta sake bude sansanin ta na Maiduguri, tunda za a iya cewa an samu zaman lafiya a jihar.

KU KARANTA: Allah ne ya yi fushi damu da cutar sankarau - Gwamna

“Yanzu an samu zaman lafiya a jihar, don haka za mu so mu sake dawowa mu bude sansanin mu. Sai dai kuma kada ku manta, har yanzu ‘yan gudun hijira na nan damfare a sansanin masu bauta wa kasa din.” Inji Kazaure.

Ya kara da cewa za a bude sansanin da zarar an kwashe ‘yan hijirar da ke zaune a cikin sansanin.

“A jihar Barno ne kadai NYSC ba su cikin na su sansanin. Amma a shirye muke a duk lokacin da gwamnatin jihar Barno ta damka mana sansanin na mu, to za mu yi gaggawar kawo masu bautar kasa da suka kammala jami’o’i a ciki.”

A karshe Kazaure ya jinjina wa masu bautar kasa da ke gudanar da ayyukan su a jihar, saboda kwazon su da kuma nuna juriya.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai wasu yan bautar kasar ne ke wani taro

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel