Yakin basasa na neman barkewa a majalisar tarayya

Yakin basasa na neman barkewa a majalisar tarayya

Akwai Alamun Raba Gari tsakain Majalisar Wakilan Nigeriya da ta Dattawa akan takun sakar dake tsakanin Majalisar Dattawan Fadar Shugaban Nigeriya.

Bukola Saraki

Bukola Saraki

Tun bayan kin amincewa da Ibrahim Magu, a matsayin shugaban hukumar yaki da masu bata dukiyar kasa ta EFCC, da shugaba Buhari, ya turawa majalisar har sau Biyu, ‘yan majalisar dattawan ke shan suka daga ‘yan Najeriya.

NAIJ.com ta samu labarin cewa, dan kwamitin kasafin kudi a majalisar wakilan Najeriya, Hon. Shehu Sale Rijau, ya ce bashi tare da abinda ‘yan majalisar dattawan suke yi, domin shugaban kasa keda hurumin kawo wanda yaga ya dace, dan haka shi ya ce yana bayan shugaba Buhari, domin ya tabbatar da yana yunkurin aiwatar da gaskiya ne.

KU KARANTA: Sarkin musulmi ya gargadi yan siyasa

Bisa dukkan alamu majalisar wakilai na shirin takawa majalisar dattijan burki biyo bayan kin tantance kwamishinonin hukumar zabe da shugaba Buhari ya turawa majalisar dattawan kamar yadda Shehu Sale Rijau, ya yi karin bayani.

Shugaban kwamitin labarai a majalisar dattawan Hon. Aliyu Sabe Abdullahi, ya ce surutan da ake yi akan su harma da zanga zangar nuna adawa da su duk ba wani bakon abu bane a siyasa, domin duk abinda za a yi sai wani ya ce bai yi masa ba dai-dai ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma wani matashi ne ke nuna rashin jin dadin sa game da jam'iyyar APC

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras
NAIJ.com
Mailfire view pixel