Allah ya kyauta: Ka ji abin da wata uwa tayi wa ‘dan cikin ta?

Allah ya kyauta: Ka ji abin da wata uwa tayi wa ‘dan cikin ta?

A wannan zamani da ake ciki na kimiyya da fasaha an gano yadda wata mahaifiya ta jefar da jinjirin da ta Haifa a cikin bola saboda tsabar rashin imani

Allah ya kyauta: Ka ji abin da wata uwa tayi wa ‘dan cikin ta?

Ta jefar da jinjirin da haifa a bola; Ashe an dauki hoton ta

NAIJ.com na da labarin yadda wata matashiyar uwa a can kasar Sin watau China ta jefar da jinjirin da ta haifa a cikin kwandon shara. A wannan zamani na fasaha dai tuni aka kama ta a dalilin na’urar daukar hoto na CCTV.

Wannan mata dai da ta fito daga Garin Shenzen da ke kasar China ta tashi ne takanas a Ranar Asabar ta jefa jinjirin ta da ke cikin wani akwati a cikin bolar shara. Wani mai shara ne dai ya tsinci jinjirin tsamo-tsamo cikin jini amma da ran sa.

KU KARANTA: Allah ne ya kawo sankarau Inji wani Gwamna

An dai wuce da jinjirin asibiti a dalilin rauni da ya samu a daidai idanun sa nan dai aka duba sa. Daga baya kuma Jami’an ‘Yan Sanda su ka binciko wanda ya jefar da wannan jinjiri nan take su ka far ma gidan wannan mata kuma aka kama ta tsamo-tsamo.

A Najeriya kuwa an daurewa wani shugaban makaranta a Jihar Kano hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari bayan an same sa da laifin kwanciya da kananan yara 2 a ofishin sa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wata mata ta koka da rashin 'ya 'ya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel