Tofa: Malaman Jami'a za su shiga yajin aiki

Tofa: Malaman Jami'a za su shiga yajin aiki

– Kungiyar ASUU ta Malaman Jami’o’i na shirin yin yajin aiki na mako guda

– Bangaren Jami’ar Ibadan ne dai ke wannan shiri

– Kungiyar ASUU tace ana zaftare mata albashi haka kurum

Tofa: Malaman Jami'a za su shiga yajin aiki

An saba: ASUU za ta shiga yajin aiki

Kungiyar ASUU ta malaman Jami’ar Ibadan za ta shiga yajin aiki a daren yau kamar yadda NAIJ.com ke samun labari yanzu haka. Kungiyar tace yajin na mako daya ne kurum domin gargadi.

ASUU ta ke cewa daga dalilan da zai za su shiga wannan yajin aiki shi ne ana zaftare masu albashi hakanan babu gaira-babu dalili. Bugu-da-kari kuma ma dai ba a biyan su wasu alawus da su ka dace.

KU KARANTA: Musulmai sun hana Fayose gina masallaci

Tofa: Malaman Jami'a za su shiga yajin aiki

ASUU: Jami’ar Ibadan za ta shiga yajin aiki a yau

Malaman Jami’ar za su shiga yaji ne daga tsakiyar daren yau har zuwa mako mai zuwa war haka. Shugaban Malaman Jami’ar na Jami’ar ta Ibadan Dr. Deji Omole ya tabbatar da wannan a taron da aka yi a Ranar Talata.

Kwanaki ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin wani kwamiti mai dauke da Mutane 14 domin zama a gana da Kungiyar ASUU ta Malaman Jami’a na kasa da kuma Kungiyoyin SSANU da NAAT da kuma NASU na Jami’o’i.

Ku same mu a Tuwita http://twitter.com/naijcomhausa ko kuma Facebook

https://www.facebook.com/naijcomhausa

Rikicin kabilanci a Jihar Osun

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel