Rahama Sadau ta ƙaro wulaƙanci: Kalli wasu kyawawan Hotunan ta

Rahama Sadau ta ƙaro wulaƙanci: Kalli wasu kyawawan Hotunan ta

Fitacciyar jarumar Kannywood da aka fi sani da suna Fina finan Hausa, Rahama Sadau ta sake sakin wasu zafafan hotunan ta sanye da wasu kayatattun kayan ado da kwalliya.

Rahama Sadau ta ƙaro wulaƙanci: Kalli wasu kyawawan Hotunan ta
Rahama Sadau

Kamar yadda Legit.ng ta ruwaito, Rahama mai shekaru 23 ta dauki hoton ne sanye da wasu irin kayan turawa tare da bakin damara data daure kwankwasonta da shi.

KU KARANTA: ‘Ina so Buhari ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2019’ – El-Rufai

Rahama Sadau ta ƙaro wulaƙanci: Kalli wasu kyawawan Hotunan ta
Rahama Sadau

Idan za’a iya tunawa a shekarar data gabata ne dai hukumar yan wasan Hausa ta dakatar da Rahama Sadau daga shirya fina finai sakamakon wani bidiyon waka data fito a ciki na wani mawaki Classiq, inda hukumar tayi zargin anyi rungume rungume a cikin bidiyon.

Sai dai duk da wannan dakatarwa da aka yi ma Rahama, bata yi kasa a gwiwa ba, ta yadda hukuncin ya zame mata tamkar gobarar titi a Jos, sakamakon gayyata data samu zuwa kasar Amurka daga fitaccen mawakin nan Akon.

Amma zuwa yanzu ba'a tabbatar da ko hukumar shirya fina finan zasu dawo da Rahama ba ko a'a. lokaci ne kadai zai iya tabbatar da hakan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon wasu yan mata da suke gargadin yan Arewa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel