Fayose na shirin rusa masallaci a jihar Ekiti

Fayose na shirin rusa masallaci a jihar Ekiti

An samu wata tashin hankali a jihar ekiti yau Talata yayinda Musulmai sukayi ca akan kokarin rusa masallacin da ke unguwan Adebayo a Ado Ekiti

Baka Isa ka rusa mana masallaci ba – Musulman jihar Ekiti ga Fayose

Baka Isa ka rusa mana masallaci ba – Musulman jihar Ekiti ga Fayose

Musulman karkashin jagorancin kungiyar National Council of Muslim Youth Organisations (NACOMYO), tace wannan shirin zaluntansu gwamnatin Fayose ke yi.

Game da cewan su, wani dillalin man fetur, Alhaji Suleman Akinbami ne ya Gina masallacin a gidan man sa kuma ya baiwa juma’a.

KU KARANTA: An kona gidan mawaki Rarara akan wakan Ganduje

An samu labarin cewa kwamishanan filin jihar, Mr Taiwo Otitoju, yaje masallacin ranan litinin domin zane cewa a rusa sa. Dalilin sa shine, warin man fetur zai Iya janyowa masu sallah ciwon daji.

Matasan sun taka daga masallacin da ke Oja Oba zuwa Odo Ado domin fadawa limamin Ekiti, Alhaji Jamiu Kewulere, kafin suka karasa fadar sarkin Ewi, Oba Rufus Adeyemo Adejugbe.

Yayinda limamin yayi musu magana, yace zai cigaba da tattaunawa da gwamnati har sai an samu sauki akan maganan.

Shugaban kungiyar NACOMYO a Ekiti, Barr Tajudeen Ahmed, ya siffanta wannan al’amari a matsayin cin zarafi. Duk da cewan yaki nada musulmai a gwamnatinsa, yana son rusa musu masallaci.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?_rdr#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel