Gobara ta lashe sashin kuɗi na gidan gwamnatin jihar Ebonyi

Gobara ta lashe sashin kuɗi na gidan gwamnatin jihar Ebonyi

Sashin kudi na fadar gwamnatin jihar Ebonyi ya babbake sakamakon wata gobara data taso daga daya cikin ofisoshin wannan barayin gidan gwamnatin.

Gobara ta lashe sashin kuɗi na gidan gwamnatin jihar Ebonyi

Motar kashe gobara a gidan gwamnatin jihar Ebonyi

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito gobarar ta fara ne da misalin karfe 9 na safe, sai dai ba’a samu asarar rai ko daya ba, kamar yadda mashawarcin gwamnan jihar kan lamurran tsaro, Kenneth Ugbala ya shaida ma NAN.

KU KARANTA: Ya tura ya yaransa 2 Almajiranci saboda ya ƙaro Amarya

Ugbala yace: “Gobarar ta samo asali ne sakamakon matsalar wasu wayoyin lantarki da aka samu a sashin kudi na gidan gwamnati, amma dai barnar da tayi takaikacce ne. sai dai wutar ta kona wasu labulaye a sashin, amma ba zamu tabbatar da asarar da aka yi ba har sai yan kwana kwana sun kammala aikinsu.”

Majiyar NAIJ.com da lamarin ya faru a gabanta tace sun dai kawai sun ga wani bakin hayaki na fitowa daga sashin kudi.

“Nan da nan sai aka fara ihun a kawo tallafi, nan fa ma’aikata suka fara amfani da ruwan kumfa suna watsawa, kafin zuwa jami’an kashe wuta,” inji majiyar.

Shugaban hukumar kashe gobara na jihar Ebonyi James Owoh yace jami’an hukumar sun yi gaggawa wajen kai agaji ga inda gobarar ta taso a fadar gwamnatin jihar.

“A koda yaushe bama yin kasa a gwiwa wajen kashe gobara, hakan yasa muka yi azama wajen rugawa gidan gwamnati a lokacin da muka samu labarin tashin gobarar, kuma aka samu nasara muka kashe wutan,” inji Owoh.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga wasu mata da suka yi zanga zanga har zuwa fadar gwamnatin jihar Legas

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel