Kasar Birtaniya za ta falasa koi; Za ta bayyana dukiyoyin ‘yan Najeriya da ke kasar a 2018

Kasar Birtaniya za ta falasa koi; Za ta bayyana dukiyoyin ‘yan Najeriya da ke kasar a 2018

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa kasar Birtaniya ta yi alkawarin cewa a shekara 2018 za ta samar wa Najeriya bayanai game da wadanda suka mallaki dukiyoyi a kasar.

Gwamnatin Birtaniya za ta ba gwamnatin tarayyar Najeriya jikakken bayani game da 'yan Najeriya da suka mallaki dukiyoyi a kasar a shekara mai zuwa 2018.

Farfesa Bolaji Owosanoye, babban sakataren kwamitin ba shugaban kasa shawarwari kan cin hanci da rashawa ya shaida wa wakilin mu na NAIJ.COM cewa tattaunawa ta yi nisa kan wannan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Mashawarcin shugaba Buhari ya ɗau alwashin maka Saraki a kotu, me yayi zafi?

Owosanoye ya ce: "Muna bukatar mu tabbatar da cewa babu wajen buya ga barayin gwamnati.”

Ya ce kasar Birtaniya ta yi alkawarin cewa a shekara 2018 za ta samar wa Najeriya bayanai game da wadanda suka mallaki dukiyoyi da kuma inda suke; wannan zai taimaka sosai.

Owosanoye ya kara da cewa bincike ta nuna cewa kimanin kashi 60 bisa dari na kudadin da ake fitarwa daga kasashen Afirka zuwa kasashen waje sun kasance daga kasar Najeriya ne saboda girman tattalin arzikin kasar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin magudi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel