Zan tabbatar an hukunta wanda ya yi wa yarinya fyade Neja - Aisha Buhari

Zan tabbatar an hukunta wanda ya yi wa yarinya fyade Neja - Aisha Buhari

- Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya Aisha Buhari ta bayyana cewar za ta tabbatar da ganin an yi wa yarinyar nan mai kimanin shekaru 16 da mataimakin shugaban makarantar sakandire ya yi wa fyade a jihar Neja adalci

- Wannan na zuwa ne yayin zaman kotun da aka yi a yau Litinin a gaban Mai Shari’a Fati Auna a Minna

Aisha Buhari

Aisha Buhari

NAIJ.com ta samu labarin cewa yarinyar da take karatu a makarantar sakandiren Tunga Minna, ta gamu da iftila’i a hannun mataimakin shugaban makarantar Muhammad Muhammad, wanda ya yi mata fyada kwanakin baya.

Majiyarmu ta nakalto cewar, Uwargidan Shugaban Kasar ta kira Matar Gwamnan Neja, inda ta bukace ta da lallai ta sanya a yi bincike don gano ainihin yadda abin ya faru, sannan a yi wa yarinyar adalci.

KU KARANTA: Matasa sun mamaye majalisa saboda Ndume

Mai magana da yawun Uwargidan Gwamnan Neja, Aisha Wakaso ta ce, an bawa Babban Daraktan Hukumar Kula da Hakkin Yara umarni ya yi bincike don tabbatar da ganin an bawa mai hakki hakkinsa.

Tuni dai aka yi wa bangaren shari’a na Hukumar bayanin komai don su san ta inda za su fara.

Kotun majistiri ta garin Minna, tana zargin Muhammad Muhammad da karya dokar sashe na 19 da na 25, na Kundin Kare Hakkin Yara.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Fati Auna, ta dage sauraron karar zuwa ranar Laraba, 5 ga watan Afrilu, inda ta bada umarni a kai wanda ake zargi gidan kaso.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma wasu mata ne ke nuna goyon bayan su ga Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel