'Yadda Boko Haram ta raba mu da gatanmu har abada' (Hotuna)

'Yadda Boko Haram ta raba mu da gatanmu har abada' (Hotuna)

- Mata wadanda Boko Haram suka kashe mazajensu na fama da tsananin rayuwa da 'ya'yansu a sansanin daban-daban

- Wasu daga matan sun kasance tare da kananan yara musammam a Maiduguri babban birnin jihar Borno

'Yadda Boko Haram ta raba mu da gatanmu har abada' (Hotuna)
Wasu mata wadanda 'yan Boko Haram suka kashe mazajensu na cikin halin kunci

Hare-Haren Boko Haram musammam a Maiduguri babban birnin jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya sun haifar da dubban marayu da kuma matan da aka kashe mazajensu aka bar su da dawainiya.

Akwai dumbin mata da kananan yara musammam a Maiduguri, da ke cikin halin tagayyara sakamakon raba su da mazan da suka dogara da su wajen kula da rayuwarsu da ta 'ya'yansu.

'Yadda Boko Haram ta raba mu da gatanmu har abada' (Hotuna)
Wata mata da 'yan marayu da aka barta da su

Legit.ng ta gano cewa akasarin wadannan mata ba su da aikin yi, ko wata sana'a, lamarin da ta tilasta wa wasunsu yin barace-barace don neman abin da za su ciyar da kansu da 'ya'yansu.

KU KARANTA KUMA: Boko Haram su yi wani sabon bidiyo

'Yadda Boko Haram ta raba mu da gatanmu har abada' (Hotuna)
Wata daga cikin matan da ke sansanonin 'yan gudun hijira na yin wasu sana'oi

Wata cikin wadannan matan na cewa ba za ta taba manta halin da ta samu kanta a ciki ba shekaru 3 da suka gabata lokacin da yan Boko Haram suka hallaka mijinta gami da 'ya'yanta 3.

Wadannan mata da Boko Haram ta raba da mazajensu na cikin tsananin buƙatar abinci da kula da lafiya da kuma ilmi ga 'ya'yansu, baya ga tallafi don samun yadda za su iya tsayawa da kafafunsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon wasu yara wadanda rikicin kudancin Kaduna ta rusa da iyayensu

Asali: Legit.ng

Online view pixel