Rundunar sojin Najeriya ta cafke mutum 2, ta bankado matatar mai a 'kudu'

Rundunar sojin Najeriya ta cafke mutum 2, ta bankado matatar mai a 'kudu'

Rundurar sojojin Najeriya ta hudu dake a garin Bennin na jihar Edo ta samu nasarar cafke mutane 2 da zargin sun kafa wata matatar mai ta boge a karamar hukumar Uhunmwode cikin wani kauye da ake kira Obazagbon.

Tsageran Neja Delta

Tsageran Neja Delta

NAIJ.com ta samu labarin cewa kusan sama da litar danyen mai 300,000 ne sojojin suka samu tare da lalatawa a matatar man.

Bayanan da aka tattaro sun nuna cewa mutanen bata gari suna fasa fayif din hukumar dake kula da matatun Najeriya watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) inda kuma suke tsiyaye danyen man.

KU KARANTA: Wata kungiya ta maka Buhari kotu

A wani labarin kuma, Daliban jami’ar jihar Kaduna KASU sun gudanar da zanga-zanga jiya a kofar shiga makarantar domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda hukumar makarantar take nuna halin ko-in-kula wajen samar wa daliban tsaro yadda ya kamata a makarantar.

Daliban sun koma da yadda ‘yan daba suka addabesu a makarantar kuma babu wani himma daga hukumar jami’ar na ganin ta samar wa daliban tsaro.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan ma dai ana bayanin yadda rikici ya barke ne tsakanin arewa da kudu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel