Tsohon gwamna na jihar Jigawa Sule Lamido yace ba zai iya shiru, mai yake so ya fada?

Tsohon gwamna na jihar Jigawa Sule Lamido yace ba zai iya shiru, mai yake so ya fada?

- Yana shirye ya hada hannu da ‘yan kishi Najeriya domin hana wannan gwamnati dake kan mulki

- Wani taro da aka gudanar a gidan shi (Bamaina ‘country home’), a karamar hukumar Birnin Kudu

- A halin yanzu gwamnati ya gaza kan matsawa da kasa gaba

Sule Lamido na cewa, ba za iya rufe mishi baki kar ya yi magana

Sule Lamido na cewa, ba za iya rufe mishi baki kar ya yi magana

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi alwashi a ranar Lahadi cewa zai yi adawa da duk wani tursasawa ko barazana da gwamnati na yanzu zai yi amfani da garin sa shi ya yi shiru.

Yadda NAIJ.com ya ruwaito, Lamido ya bayyana haka ne yayin jawabi ga mambobi jami’yyar PDP na Jihar Jigawa a wani taro da aka gudanar a gidan shi (Bamaina ‘country home’), a karamar hukumar Birnin Kudu.

KU KARANTA: Gwamatin tarayya zata fara rijistan matasa maras aiki gobe Laraba

Ya ce yana shirye ya hada hannu da ‘yan kishin Najeriya domin hana wannan gwamnati dake kan mulki, wajen sa mutane su yi shirun dole ta hanyar tursasawa.

Tsohon gwamnan ya ce yadda talauci ke damun al'ummar kasar yanzu ya bayyana rashin iya rike kasa da kyau na gwamnatin yanzu. "Ingancin shugabanci na APC ya ‘kife jirgin ruwan’ ne saboda rashin shugabanci.

KU KARANTA: Tsohon dan takaran gwamna a PDP, da mutane 500 sun sheke APC

“A halin yanzu gwamnati ya gaza kan matsawa da kasa gaba, a maimakon haka, duk al'amurran na cigaban dan Adam suna koma baya," ya riya.

Lamido, wanda yana facaka abubuwa da ya yi a jihar da a matsayin gwamnan. Ya nuna takaici kan abin da ya bayyana a matsayin "matalautar jagorancin" daga wanda jihar kai fama a yanzu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan Bidiyo na tambaya a duk 'yan siyasa, wanda shi ne ba ya cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel