Rigiji-gabji: An maka Gwamnatin shugaban Buhari a kotu

Rigiji-gabji: An maka Gwamnatin shugaban Buhari a kotu

Wata Kungiya mai suna SERAP ta maka Gwamnatin shugaba Buhari a Kotu inda ta ke nema a ji yadda kowace Jiha ke kashe bashin nan da aka maido masu kwanan nan

Rigiji-gabji: An maka Gwamnatin shugaban Buhari a kotu

shugaba Buhari da Gwamnonin Jihohi

Kungiyar SERAP mai kokarin ganin yadda Gwamnonin Jihohi 35 da aka aikawa bashin da aka maido su ka kashe kduin. Kungiyar na nema ta ga yadda kowane Gwamna ya kashe wannan makudan kudi da ya kusa Naira Biliyan 400.

Akwai rade-radin cewa Gwamnonin sun barnatar da kudin ne a banza ba su yi aikin da ya dace ba. Dalilin haka ne SERAP mai kokarin ganin an yi gaskiya-da-gaskiya ta maka Gwamnatin kasar a babban kotun tarayya na Legas.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta fara rajistar marasa aikin yi

Rigiji-gabji: An maka Gwamnatin shugaban Buhari a kotu

Gwamnonin Najeriya a wani taro da shugaban kasa

Kungiyar SERAP na nema a tilastawa Akanta-janar na kasar Alhaji Idris Ahmed da kuma Ministan shari’a Abubakar Malami su fito da bayani ga duniya daki-daki game da yadda kowane Gwamna ya kashe wannan kudi. Sai dai har yanzu ba a sa ranar fara shari’ar ba tukun.

NAIJ.com ta kuma kawo maku rahoto cewa bisa dukkanin alamu shugaban kasa bai da niyyar cire Ibrahim Magu daga matsayin sa duk da cewa Majalisa ta ki tabbatar da shi ba ma sau daya ba.

KU KARANTA: Gwamnati na nema a kama tsohon Ministan shari'a

Rigiji-gabji: An maka Gwamnatin shugaban Buhari a kotu

An maka Gwamnatin Buhari a gaban kuliya

Kudin da kowace Jiha ta lashe:

Akwa Ibom N14.5bn; Bayelsa N14.5bn; Delta N14.5bn; Kaduna N14.3bn; Katsina N14,5bn; Lagos N14.5bn; Rivers N14.5bn; Borno N13,654138,849.49. Imo 13bn; Jigawa 13.2bn; Niger N13.4bn; Bauchi N12.7bn. Benue N12.7bn, Anambra N11.3bn; Cross River N11.3bn8; Edo N11.3bn; Kebbi N11bn; Kogi N11.2bn; Osun N11.7bn; Sokoto N11.9bn; Abia N10.6bn; Ogun N10.6bn; Plateau N10.4bn; Yobe N10bn; Zamfara N10bn. Adamawa N4.8bn; Ebonyi N3.3bn; Ekiti N8.8bn; Enugu N9.9bn; Gombe N8.3bn; Kwara N5.4bn; Nasarawa N8.4bn; Ondo N6.5bn; Oyo N7.2bn. Taraba N4.2bn.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani mutumi yayi kaca-kaca da Jam'iyyar APC mai mulki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda

Kungiyar tsaro na farar hula ta bukaci a daure Sufeto Janar na ‘yan sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel