Saraki yace babu wani rikici tsakanin su da Buhari

Saraki yace babu wani rikici tsakanin su da Buhari

- Saraki yace dan majalisa taki tabbatar da wasu sunaye da Shugaba Buhari ya gabatar, ba wai ana sa'insa bane

- Yace alakar majalisan da fadar Shugaban kasa na nan da kyau, babu wani rikici tsakanin su

- Kana Saraki ya bada tabbacin cewa majalisan zata zauna domin tabbatar da ministocin da Shugaba Buhari ya gabatar.

Zamu zauna domin tabbatar da ministocin da Buhari ya gabatar - Saraki

Saraki

Shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, yace zasu cigaba da zaman majalisa domin tabbatar da ministocin da Shugaba Buhari ya gabatar makon da ya gabata

Saraki yace dan majalisa ta dakatad da zaman tabbatar da wasu kwamishanonin hukumar INEC, ba wai tana sa'insa da fadar Shugaban kasa bane.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da shugabannin majalisa

Jaridar This day ta bada rahoton cewa Saraki yace har yanzu akwai kyakkyawan alaka tsakanin bangarorin biyu.

Yace: " Munada alaka mai kyau. Ba zaka Iya cewa muna sa'insa akan zancen NDDC ko EFCC ba. Akwai sauran abubuwa a gabanmu. Munada aikin tabbatar da ministoci wanda zamuyi.

“Munada aikin kasafin kudi wanda yafi muhimmanci . Munada INEC,PIB, munada abubuwa masu amfani da yawa da ke gabanmu.

“Kamar yadda na fada , wannan ganawar da muka Saba ne. Akwai wasu abubuwa mafi muhimmanci ma misali kasafin kudin kasa. Munyi magana akan dokar INEC din da muka zantar."

A bangare guda, jaridar NAIJ.com ta tattaro muku cewa sanatocin jami'yyar PDP sun tuhumci babban jigon jami'yyar APC, Bola Tinubu, da cewa yana zagon kasan sanatoci tare da hukumar EFCC.

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel