Tafiyar Buhari na ganin likita ya kasance cin hanci da rashawa – Fasto Chukwuma

Tafiyar Buhari na ganin likita ya kasance cin hanci da rashawa – Fasto Chukwuma

- Babban fasto na cocin katolika dakeEnugu, Rev Emmanuel Chukwuma yace shirin da shugaban kasa Buhari keyi na komawa kasar waje don ci gaba da magani ya kasance ba’a ga gangamin da gwamnatin sa keyi na canji ya fara da ni

- Fasto Chukwuma ya bada shawarar cewa a maimakon tafiya kasar waje don magani, a shigo da kayayyakin aikin da ake amfani gurin yima shugaban kasa magani zuwa Najeriya don yi masa amfani da su a gida

- Malamin yayi kira ga shugaban kasa da ya yi imani da hukumomin kiwon lafiya dake Najeriya

Tafiyar Buhari na ganin likita ya kasance cin hanci da rashawa – Bishop Chukwuma

Fasto Chukwuma ya shawarci shugaban kasa da ya yi imani da hukumomin kiwon lafiya dake Najeriya

Babban fasto na cocin katolika dakeEnugu, Rev Emmanuel Chukwuma yace shirin da shugaban kasa Buhari keyi na komawa birnin Landan don ci gaba da magani, cin hanci da rashawa ne.

KU KARANTA KUMA: Labari da Dumi-Dumi: Boko Haram su yi wani sabon bidiyo

Da yake magana a gurin taron coci, Fasto Chukwuma yace tafiyar ganin likitan Buhari a kasar waje ba’a ne ga gangamin gwamnatin san a canji ya fara da ni, jaridar Guardian ta ruwaito.

NAIJ.com ta rahoto inda malamin yace bai goyi bayan shirin tafiya ganin likitan ba, musamman kamar yadda kasar ke cikin wani hali na koma bayan tattalin arziki.

Fasto din ya bada shawarar cewa a maimakon tafiya kasar waje don magani, a shigo da kayayyakin aikin da ake amfani gurin yima shugaban kasa magani zuwa Najeriya don yi masa amfani da su a gida.

KU KARANTA KUMA: EFCC: Shugaban kasa ba zai sauke Ibrahim Magu baEFCC: Shugaban kasa ba zai sauke Ibrahim Magu ba

Ya ce shugaban kasa da ya yi imani da hukumomin kiwon lafiya dake Najeriya, sannan kuma yayi amfani da kasafin kudin 2017 gurin bunkasa ma’aikatar lafiya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon da aka bukaci yan Najeriya da su ambaci yan siyasa masu cin hanci da rashawa.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel