EFCC: An kama na kusa da tsohon shugaba Jonathan

EFCC: An kama na kusa da tsohon shugaba Jonathan

An fara zama a game da shari’ar wani na kusa da tsohon shugaban kasar nan Jonathan Goodluck. Ana zargin Warpamo Dudafa da yin gaba da wasu miliyon daloli

EFCC: An kama na kusa da tsohon shugaba Jonathan

EFCC ta damke Dudafa

Alkali B. Kuewumi na babban Kotun tarayya da ke Garin Legas ya fara karban wasu shaida a game da shari’ar wani mai ba tsohon shugaban kasa Jonathan shawara a kan harkokin cikin gida a lokacin da ya ke mulki.

EFCC na zargin Mista Warpamo Dudafa da wasu mutane 6 da yin gaba da kudi har Dala miliyan 15 kamar yadda NAIJ.com ke samun labari. Hukumar EFCC dai ta maka na kusa da Jonathan din ne a Kotu kan wasu laifuffuka 15.

KU KARANTA: Buhari ya toshe wata hanyar sata a Najeriya

EFCC: An kama na kusa da tsohon shugaba Jonathan

EFCC: Dudafa ya shiga uku ya lalace

Sauran wadanda EFCC ta ke zargi sun hada da Amajuoyi Briggs da Adedamola Bolodeokua. Tuni dai hukumar ta fara bada shaidun asusun bankin da ke nuna cewa ba shakka wadannan mutane sun yi awon gaba da kudi.

Haka kuma dai bisa dukkan alamu Sanatan nan watau Dino Melaye da ake ta magana a kan sa kwanaki a dalilin wasu zargi ya kara shiga wata matsalar yanzu haka don kuwa yana da asusu a bankunan kasar waje wanda hakan bai halatta ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An damke wani tsohon shugaban NNPC a kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel