Idanun Chelsea da Man Utd sun rufe a ƙoƙarinsu na siyan ƙwararren ɗan ƙwallon Najeriya

Idanun Chelsea da Man Utd sun rufe a ƙoƙarinsu na siyan ƙwararren ɗan ƙwallon Najeriya

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da na Manchester United sun nuna muradin siyan dan wasan Najeriya mai tasowa Moses Simon, kuma ana sa ran daya daga cikinsu zai dauke shi daga kungiyarsa ta Gent.

Idanun Chelsea da Man Utd sun rufe a ƙoƙarinsu na siyan ƙwararren ɗan ƙwallon Najeriya

Moses Simon

Wasu bayanai da suka ishe NAIJ.com shine kungiyoyin biyu sun tura wakilansu suje su gani yadda Moses ke taka leda a can kasar Beljam inda yake gudanar da sana’arsa a karshen makon data gabata, inda a yayin wasn da suka buga Moses ya zura kwallaye har guda biyu.

KU KARANTA: Real Madrid da Barcelona sun kafa tarihi

Moses ya zura kwalle biyun ne a wasan su da kungiyar Club Brugge a ranar Lahadi 2 ga watan Afrilu, rahotanni sun bayyana cewar wakilan kungiyoyin sun gamsu da taka ledar Moses,sai dai ba’a tabbatar da ko sun samu ganawa da shi ba.

Dama dai mai horar da kungiyar Chelsea Antonio Conte yana neman dan wasan da zai iya buga guraben kwallo da dama, yayin da shi kuma Mourinho yake neman dna wasan da zai maye gurbin Zlatan Ibarhimovic idan ya yanke shawarar tafiya a karshen kakan wasa.

A wani hannun kuma dan wasa Moses Simon ya zura kwallaye biyu kenan a wasanni 24 da ya buga ma kungiyar Gent.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli yadda kungiyar kwallo kafa ta Najeriya ke gudanar da atisayen fafatawa don samun gurbin shiga gasar kofin duniya na badi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel