RA’AYOYIN JAMA’A: ‘Duk ɗan siyasan Najeriya ɓarawo ne’ inji ýan Najeriya

RA’AYOYIN JAMA’A: ‘Duk ɗan siyasan Najeriya ɓarawo ne’ inji ýan Najeriya

Wakilin NAIJ.com ya zagaya unguwannin jihar Legas don jin menene ra’ayin yan Najeriya dangane da yan siyasan Najeriya?

Yawancin wadanda suka amsa tambayar nan sun bayyana cewa dukkanin shuwagabannin siyasan Najeriya nada kashi a tare dasu irin na sata, almundahana, cin hanci da rashawa.

KU KARANTA: Fashola ya lashe kyautan gwarzon minista a Najeriya

Biyo bayan tashi haikan da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wajen yaki da cin hanci da rashawa ba tare da nuna sani ko sabo ba, hakan ya hako jama'a da dama da ake zargi da aikata wani laifin handama da babakere ko kuma na cin hanci da rashawa.

Da dama daga cikin mutanen da suka rike madafan mulki a gwamnatin data gabata an kama su da hannu dumu dudmu cikin badakaloli da dama na makudan kudaden gwamnati, kama daga badakalar kudin man fetur, ko badakalar tallafin man fetur, zuwa badakalar kudin makamai.

Ko a yan kwanakin da suka gabata sai da hukumar EFCC ta gano wasu makafin kudaden da aka boye a wani gidan tsohon shugaban hukumar matatan man fetur, NNPC Andrew Yakubu, kuma a yanzu haka yana fuskantar shari'a gaban kuliya manta sabo.

Hakazalika shima tsohon gwamnan jihar Adamawa Bala Ngilari ya gamu da fushin kotu sakamakon kama shi da laifi da tayi da yi ma dokar siyayyan a gwamnatance zagon kasa. a bangaren majalisar dokokin kasar nan ma da dama daga cikin sanatoci suna fuskantar shari'u gaban kotuna daban daban kan laifukan almundahana.

wannan ne ya sanya yan Najeriya yi ma shuwagabannin siyasar Najeriya kudin goro, inda wasu ke ganin muddin aka tsananta bincike toh tabbas babu wanda zai sha a cikinsu, don kuwa dukkanin suna da kashi a kutirinsu.

Ku kalli bidiyon ra’ayoyin a nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon Andrew Yakubu a gaban Kotu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel