Shugaba Buhari ya jajintawa iyalan wadanda suka hallaka sanadiyar ciwon sankarau

Shugaba Buhari ya jajintawa iyalan wadanda suka hallaka sanadiyar ciwon sankarau

Shugaba Muhammadu Buhari ya jajintwa iyalan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyar ballewan ciwon sankarau musamman a arewacin Najeriya

Shugaba Buhari ya jajintawa iyalan wadanda suka hallaka sanadiyar ciwon sankarau

Shugaba Buhari ya jajintawa iyalan wadanda suka hallaka sanadiyar ciwon sankarau

Akalla mutane 300 sun rasa rayukansu cikin wata 1 da ya gabata.

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya mia sakon shugaba Buhari ne yayinda ya je ta’aziyya kauyen Danchai a karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto.

A jihar Sokoto kadai, akalla mutane 41 ne suka hallaka.

KU KARANTA: Matasa sunyiwa barawon babur lillis

Yace: “Shugabanmu Muhammadu Buhari, yace in mika sakon ta’aziyyarsa gareku. Yace kuma suna daukan matakin dakile wannan annoba saboda kada ya sake faruwa."

“An turo jami’an bada lafiya kuma suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da lafiyanku."

“Muna kira da ku cewa ku bi umurni da kuma hada kai da mu wajen shawo kan wannan kalubale."

Ya kara da cewa sama da mutane 700,000 za’ayiwa riga kafi a kananan hukumomi 23 a jihar.

Jaridar NAIJ.com ta baku rahoton cewa mutane da dama sun hallaka a jihar Zamfara bisa ga yaduwan ciwon sankarau a jihar.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel