Za a fuskanci wahalar man fetur a Nigeria — Inji kungiyar NUPENG

Za a fuskanci wahalar man fetur a Nigeria — Inji kungiyar NUPENG

- Kungiyar kwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas, NUPENG ta kammala shirin shigar wani yajin aiki wanda zai iya sanadiyar wahalar man fetur a kasar

- Kungiyar ta sanar cewa ba ranar da ake zaton daina yajin aikin ba idon aka fara ta

- Kungiyar kwadagon na kokawa kan karancin albashi da lalatattun titunan a fadin kasar

A ranar Litinin, 3 ga watan Afrilu ce direbobin manyan motocin dakon man fetur za su fara yajin aiki a Najeriya.

Kungiyar kwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas NUPENG, ta ce za ta shiga yajin aikin ne saboda karancin albashi da lalatattun titunan kasar da suke bata musu motoci.

Wani mai magana da yawun kungiyar Cogent Ojobo, ya yi gargadin cewa za a fuskanci wahalar karancin man fetur da dizal da kananzir a kasar, saboda za su dakatar da rarraba su.

Kungiyar ta shaida wa NAIJ.COM cewa ba a saka ranar da ake zaton daina yajin aikin ba.

Hakan na nufin tattaunawar da aka yi tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayyar Najeriya bai yi tasirin hana kungiyar shiga yajin aikin ba.

KU KARANTA: APC zata sulhunta majalisar dattawa da shugaba Buhari

Wannan ba shi ne karo na farko da kungiyoyin kwadagon ma'aikatan man fetur ke shiga yajin aiki ba a Najeriya, kuma a duk lokacin da suka shiga to ana fuskantar matukar wahalar man a kasar.

Tun a ranar Asabar, 1 ga watan Afrilu ne hankalin 'yan kasar ya fara tashi sakamakon rade-radin yajin aikin da suka ji, inda gidajen man suka fara cika da motoci.

Mutane sun ta cika tankunan motocinsu da man, har ma suna saye a jarkoki duk saboda tanadi don tsoron fuskantar wahalar karancin man.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon zanga-zanga ma'aikatan kananan hukumomin jihar Legas

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel