Assha! Darajar Naira ta fadi da kashi 8 cikin dari

Assha! Darajar Naira ta fadi da kashi 8 cikin dari

Labaran da muke samu yanzu haka suna nune da cewa darajar Naira ta kara yin kasa da kusan kashi 8 cikin dari a kasuwannin cikiki a satin da ya gabata duk kuwa da kokarin da babban bankin kasa keyi.

Darajar Naira

Darajar Naira

Naira din dai ta sake fadowa ne yayin da ita kuma dala ta kara yin sama a kasuwannin bayan fagen da akeyin canjin kudaden.

NAIJ.com dai ta ruwato cewa a kwanakin baya dai Naira din ta kara daraja sosai inda ta kara kusan darajar kashi 30 cikin dari a cikin kwanaki 5 kacal.

Kudin na Naira dai an saida su a N370 akan kowace dala daya a farkon mako kafin daga bisani kuma tayi tashin gwaron zabi ta kai har N394 a karshen sa.

KU KARANTA: Ba zan iya maido da Ndume ba - Saraki

A wani labarin kuma, Gwamnatin jihar Kogi a jiya ta tabbatar da cewa cutar zazzabin Lassa ta bulla jihar inda kuma suka tabbatar da cewa wani mutum 1 ne ya kamu da cutar kawo yanzu.

NAIJ.com ta tsinkayi Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Saka Haruna Audu shine ya bayyana hakan a jihar inda yace an kawo wani marar lafiya ne a asibin gwamnatin tarayya dake a garin Lokoja da alamomi na cutar yana zubar da jini.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Nan kuma ga wata mace nan mai gyaran motoci

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel