Fashola ya lashe kyautan gwarzon minista a Najeriya

Fashola ya lashe kyautan gwarzon minista a Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Legas kum ministan ayyuka, lantar da gidaje a yanzu Mista Babatunde Fashila ya lashe kyautan gwarzon minista da kungiyar ‘City People’ ta sanya.

Fashola ya lashe kyautan gwarzon minista a Najeriya

Minista Fashola

NAIJ.com ta dauko muku rahoton jawabin godiya da minstan Fashola yayi a yayin taron daya gudana a ranar Lahadi 2 ga watan Afrilun 2017 a garin Legas.

A jawabinsa, Fashola yayi bayanai masu ratsa da jiki da suka kara tabbatar da shi a matsayin mutumin daya san ya kamata kuma ya dace da lashe kyautan girmamawan na kungiyar ‘City People’.

“A koda yaushe, abu ne mai sauki jama’a su zabo mutum baya daga wani rukunin abokan aiki da suke ganin yafi kwarewa a wannan rukuni, hakan ya sanya a duk shekara ake zabo gwarzon dan shekara a tsakanin yan kwallo, amma a kokarin yin haka, mukan manta da cea abu mafi muhimmanci shine yadda abokan aiki suke hada karfi da karfe wajen ganin an cimma manufa.

“Don haka, aiki tare, da samun nasara a tare yafi samun nasarar mutum daya tilo. Haka zalika ita ma gwamnati bata da wnai bambamci da kungiyar yan kwallo, ta yadda dukkaninsu suna hada kai ne don cimma wata manufa da aka sa a gaba.

“Kowane kungiya data samu nasara toh zaka cewa tana da manaja na gari, kuma sahihi, wanda shima yana tare da masu taya shi aiki, a gwamnatin mu shugaban kasa Muhamamdu Buhari ne manajan mu, kuma yana gudanar da aikin manajan yadda ya kamata, tare da abokin aikinsa mataimakin shugaban kasa wanda yana sane da nauyin dake kansa na aiki tukuru don ganin an samu canji, kuma baya nuna gazawa. A madadin su, na karbi wannan lambar yabo.

KU KARANTA: ‘Sai Buhari, babu gudu ba ja da baya’ – Tinubu

“Duk wani kwallo da dan wasan gaba ya zura a raga, ta samu ne sakamakon bani in baka da aka dinga yi tun daga gola har zuwa sauran yan wasa, don haka a kungiyar mu, dukk ministocin mu suna taimaka ma juna, muma a ma’aikatan ayyuka, gida da lantarki muna samun taimakon ma’aikatan kasafin kudi, ma’aikatan kudi tare da ofishin sakataren gwamnati, a madadinsu, na karbi wannan lambar yabo.

“Sanin kanku ne kungiya ba zata cigaba ba sai da kudi da goyon bayan masu saka hannun jari. Kuma na smau goyon bayan sosai daga majalisun dokokin kasar nan, da dukkanin shuwagabannin kwamitocin su, don haka wannan lambar yabo tasu ce, na amshe shi a madadinsu.

“Da dama cikin ayyukan mu ba zasu tafi yadda ya kamata ba da ba don kotunan kasar nan sun warware su ba, don haka na sadaukar da wannan lambar yabo ga sashin shari’ar kasar nan, na karbi wannan lambar yabo a madadinsu." Inji Fashola

Fashola ya lashe kyautan gwarzon minista a Najeriya

Fashola

Ministan yacigaba da fadin “Babu wani kungiya da zai smau nasara ba tare da kokarin wasu ma’aikata na bayan fagge, ma’aikatan mu tana da jami’ai da dama da suka hada da manyan sakatarori guda 2, daraktoci, shuwagabannin hukumomi da sauran ma’aikatan dake tallafa mana, na sadaukar da lambar yabon nan a gare su.

“Kamar yadda na fada a baya, ba za’a karrama wani dan wasa ba duk iya kwallonsa muddin kungiyarsa bata samun nasara, don haka na a madadi na da abokin aiki na karamin ministan ayyukan, gidaje da lantarki Mustapha Baba Shehuri, na amince da karbar wannan kyauta.

“Sai kuma jam’iyyar mu, APC wanda itace jirgin canji, ku sani yanzu aka fara aikin, mu kan mu mun san da haka, zamu dage wajen ganin mun samu nasara. Mun gode ma kungiyar City People da suka kara mana kaimi da kwarin gwiwa.”

Wannan shine jawabin godiya da ministan ayyuka, gidaje da lantarki Fashola yayi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ministan Buhari yace yana sauraron koken koken talakawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel