Buratai ya bayyana dabarun da suka yi amfani dasu wajen daƙile harin ýan Boko Haram

Buratai ya bayyana dabarun da suka yi amfani dasu wajen daƙile harin ýan Boko Haram

Babban hafsan sojin kasa Laftanar Janara Tukur Buratai ya bayyana dabarun yakin da suka yi amfani dasu wajen dakile hare haren Boko Haram tare da karya lagon kungiyar.

Buratai ya bayyana dabarun da suka yi amfani dasu wajen daƙile harin ýan Boko Haram

Laftanar janar Buratai

Buratai ya bayyana haka ne a ranar Lahadi 2 ga watan Afrilu inda yace sun gano wasu mafakar yan Boko Haram ne, wanda daga nan ne suke shiryawa tare da tsare hare harensu, sa’annan suka yi luguden wuta a wadannan mafaka.

Buratai ya bayyana cewar jami’an sojoji da na sauran hukumomin tsaro ne suka diran ma wadannan mafaka suka rugurguza su, yace wannan shine sanadiyyar saukin hare haren bom din da aka samu a jihar Borno gaba dayannta, kamar yadda NAIJ.com ta ruwaito.

KU KARANTA: Buratai ya jinjinawa dakarun sojin Najeriya

“Ina tabbatar muku da cewa harin bom ya ragu sosai ba kamar da ba. A kwanaki uku da suka gabata ba’a samu hari ko daya ba, muna fatan a cigaba da haka. Wata kila su yanke shawarar yin fito na fito, amma zamu tashi duk wani wajen da muke tsammanin suna wurin. Na san muna samun nasara wajen dakile hare haren bom, amma dai akwai sauran aiki.

“An wuce zamanin da yawna satar kudade ke kawo man tsaikon aiki, don haka nake shawartar jama’an jihar Borno dasu taimaka wajen tona asirin yan Boko Haram. babu yadda za’ayi ace wai yara kanana mata dauke da bom zasu san inda zasu je su kai hari ba tare da wani ye zai kais u inda zasu kai hare haren ba.

Buratai ya bayyana dabarun da suka yi amfani dasu wajen daƙile harin ýan Boko Haram

Sabbin motocin yakin sojoji

“Muna ganin akwai wasu cikin jama’a dake taikamaka musu, ko kuma wasu daga cikin yayan kungiyar da suka saje cikin jama’a suke taimaka ma yan matan wajen isar dasu inda zasu kai hari. Batun magance harin kunan bakin wake abu ne daya shafi ilimin tattara bayanai , don haka muna hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro don shawo kan matsalar,” inji Burata.

NAIJ.com ta tattaro bayanai dake nuna za’a sauya fasalin tsarin yaki na Operation Lafiya Dole a bana, Buratai yace ya zama wajibi a sauya fasalin aikin duk da yan hare haren bom din da ake fama da shi.

“Sauyin fasalin ba yana nufin za muyi kasa a gwiwa bane dangane day akin Boko Haram, zamu sauya fasalin aiki ne don inganta yanayin aikin, tare da karfafa rundunoninmu sakamakon muna kara samun kayan aiki na zamani, asali ma zamu kara kaimin yakin ne da zage damara.” Inji Buratai

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zaka tausaya ma yan gudun hijira idan ka kalli bidiyon nan:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel