Jama'a ne za su yanke hukuncin karshe kan dokar aure – Majalisar dokoki

Jama'a ne za su yanke hukuncin karshe kan dokar aure – Majalisar dokoki

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce jama'ar jihar ne za su yanke hukuncin karshe a kan kudurin dokar hana talaka futuk auren mace fiye da daya.

Jama'a ne za su yanke hukuncin ƙarshe kan dokar aure – Majalisar dokoki

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Majalisar ta ce sai ta gudanar da zaman sauraron ra'ayin jama'a don jin ko kudurin dokar auren ta dace da muradin al'ummar jihar, da zarar an gabatar mata da kundin.

KU KARANTA KUMA: An maka Bukola Saraki da wasu Sanatoci a Kotu

Shugaban majalisar, Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya ce, da ma dadin dimokradiyya kenan, don haka majalisa za ta bai wa malamai da sarakuna har ma da sauran jama'ar gari damar bayyana ra'ayoyinsu a kan kudurin dokar.

kudurin dokar auren wadda sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ke son bullo da ita na ci gaba da janyo takaddama mai zafi a ciki da wajen Kano.

NAIJ.com ta rahoto cewa kudirin ya kunshi batutuwan auratayya iri daban-daban wadanda sarki Sanusi ke ganin sun janyo tabarbarewar harkokin zamantakewa da tarbiyya.

Kabiru Rurum ya ce: "Kamar yadda al'adar gabatar da dokoki take, za a yi wa kudurin dokar karatu na daya da na biyu. Kuma hakika, na tabbatar da cewa za mu bai wa al'umma dama musammam malamai da sarakuna da su kansu ma'auratan.

"A zo a yi taro na jin ra'ayin al'umma a ga shin wannan doka ta yi daidai da abubuwan da addinin musuluncinmu ya tanada ko kuwa akwai wani abu da ake ganin ya kamata a gyara a ciki."

KU KARANTA KUMA: Sanata Ibn Na’Allah ya sha da kyar a garin ZuruSanata Ibn Na’Allah ya sha da kyar a garin Zuru

A cewarsa: "Fadar sarkin Kano ita ma al'umma suke mulka kuma su suke wakilta, wanda na tabbatar da cewa ra'ayin jama'a shi ne a gabansu.

"Na tabbatar a karshe dukkan abin da al'ummar Kano suka ga ya fi dacewa a kan wannan doka. Idan aka yi shi ita ma fada za ta goyi baya ko da ya yi daidai da ra'ayinta ko bai yi daidai da ra'ayinta ba."

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wata mata da ta koka kan rashin 'ya 'ya a duniya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili

‘Yansanda sun tsare jagoran kungiyar BBOG Oby Ezekwesili
NAIJ.com
Mailfire view pixel