‘Sai Buhari, babu gudu ba ja da baya’ – Tinubu

‘Sai Buhari, babu gudu ba ja da baya’ – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ya jaddada goyon bayansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, tare da tabbatar mai da goyon bayan dukkanin jama’an yankin yarbawa.

‘Sai Buhari, babu gudu ba ja da baya’ – Tinubu

Tinubu da Buhari

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Asabar 1 ga watan Afrilu a taron kwamitin goyon bayan Buhari wato Support Groups (NCBSG) a turance, da ya gudana a jihar Legas.

KU KARANTA: An maka Bukola Saraki da wasu Sanatoci a Kotu

Tinubu ya samu wakilcin mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen kudu masu yamma Cif Pius Akinyelure yace yana da yakinin gwamnatin Buhari ba zata gaza ba har sai ta sauya fasalin tattalin arzikin kasar nan.

“Yankin kudu maso yammacin kasar nan na goyon bayan Buhari dari bisa dari duk da kalubalen tattalin arzikin kasa da muke fuskanta, amma muna da yakinin shugaban Buhari zai magance su gaba daya, wannan tabbaci ne na cewa babu wata jam’iyyar da tayi abinda APC tayi

“Muna yin iya bakin kokarinmu duk da karancin kudade don ganin ce mun ciyar da kasar gaba, muna bukatar goyon bayan jama’a,” in ji shi.

A nasa jawabin, shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin Sanata Ajayi Borofice ya bukaci yan Najeriya dasu jajirce don ganin an kawo ma kasar cigaba ta kowanne fanni.

A wani hannun kuma NAIJ.com ta ruwaito jam’iyyar APC ta tabbatar da hukuncin dakatar da wasu shugabannin jam’iyyar na karamar hukumar Uhunmwode na jihar Legas.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani dan Najeriya yace a binne shugabannin mu gaba daya, ka yadda?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel