Allah mai iko: Kare ya ceci mutane daga hannun ‘Yan Boko Haram

Allah mai iko: Kare ya ceci mutane daga hannun ‘Yan Boko Haram

Wani kare yayi sanadiyar cecen rayuwar mutane masu dinbin yawa a Garin Borno inda ya hana wata yarinya tada bam a wani gidan biki

Allah mai iko: Kare ya ceci mutane daga hannun ‘Yan Boko Haram

Boko Haram: Kare yayi shahada?

Sai ace ko karen nan yayi mutuwar shahada kenan inda ya rasa ran sa yana kokarin kare na Jama’a? Wannan kare dai yayi sanadin karin kwanan mutane masu yawa yayin da ya hana wata yariniya harba bam a wani gidan biki.

NAIJ.com ta samu labari cewa wannan kare na wani mai gida ne a kusa da inda wannan abu ya faru. Karen dai ya hana wata ‘yar yarinya kutsawa cikin Jama’a domin ta harba bam wanda da ya ga bayan mutane da dama a cikin wani gida da ake sha’anin biki.

KU KARANTA: 'Yan kunar bakin wake sun mutu da safiyar Allah

Jami’an ‘Yan sanda su ka ce ko da karen ya hango wannan yarinya ta auka cikin Jama’a sai ya bi ta, nan fa aka yi ta kaya-kaya har bam din ya tashi, nan ne aka rasa wannan kare. Wannan abu dai ya faru ne a Garin Belbelo da ke Jihar Borno.

A Arewa dai Cutar sankarau na cigaba da yaduwa a Jihohi da dama inda yara da yawa su ke mutuwa a dalilin haka. Cutar yanzu ta auka Garin Sokoto, Zamfara, Bauchi, Katsina da ma wasu Garuruwan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin Abubuwa a kasuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel