Yan kunar bakin wake uku sun mutu a harin sassafe

Yan kunar bakin wake uku sun mutu a harin sassafe

- Yan kunar bakin wake uku na kungiyar Boko Haram sun kashe kawunan su

- Sun mutu a bam din da suka tayar da kansu a harin sassafe

- An rahoto cewa yan ta’addan sunyi yunkurin mamaye Maiduguri, babban birnin jihar Borno tare da rigunan bam a jikin su

Wasu mutane uku, wadanda ake zargin yan kunar bakin waken Boko Haram ne, sun mutu sakamakon wani harin sassafe da suka kai a ranar Lahadi, 2 ga watan Afrilu, lokacin da sukayi yunkurin tayar da Maiduguri, babban birnin jihar Borno sanye da rigunan bam a jikinsu, cewar wani jami’i.

Yan kunar bakin wake uku sun mutu a harin sassafe

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa biyu daga cikin yan kunar bakin waken sunyi yunkurin shiga birnin ta daya daga cikin sananun hanyar dake kusa da garejin Muna, wani shahararen tashar mota a hanyar Maiduguri-Gamboru.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yanke hukuncin karshe a kan Magu yayinda ya yi zaman lafiya da majalisa

NAIJ.com ta tattaro cewa basu samu shiga cikin garin ba sosai kafin wasu jami’an tsaron garin suka gano su. A take yan kunar bakin waken suka tayar da kawunan su don gudun karda a kama su. Babu wanda yam utu a harin sai yan kunar bakin waken guda biyu.

Kakakin yan sandan jihar Borno, Victor Isuku, yace wani dan kunar bakin wake shi kadai, a daidai wannan lokacin a wani guri daban a yankin, yayi kokarin kai hari gay an farin hula amma jami’an tsaro suka dakatar da shi. Dan kunar bakin waken ya kare ne da kashe kan sa da kuma jima wani dan farin hula rauni.

Yan ta’addan Boko Haram na ci gaba da kai hari ta hanyar amfani da yan kunar bakin wake wadanda ke kokarin shiga garin a sace ta hanyoyi biyu: garejin Muna a hanyar Maiduguri-Gamboru da kuma hanyar Molai babban titin Maiduguri-Biu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon wani mutumi da yayi danasanin kasancewar sa mamba a jam'iyyar APC.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel