Yadda aka hada baki da Obasanjo domin a ga bayan Abacha Inji tsohon Janar

Yadda aka hada baki da Obasanjo domin a ga bayan Abacha Inji tsohon Janar

– Janar Bamaiyi ya fasa kwan abubuwan da su ka faru a zamanin Abacha

– Bamaiyi yace Janar Abdussalami ya san da mutuwar Abiola

– Haka kuma Bamaiyi yace da hadin bakin Obasanjo aka so a kifar da Abacha

Yadda aka hada baki da Obasanjo domin a ga bayan Abacha Inji tsohon Janar
Ishiaya Bamaiyi ya fasa kwan abin da ya faru a lokacin baya

Tsohon na biyu a lokacin shugaba Marigayi Janar Sani Abacha watau Laftana-Janar Ishaya Bamaiyi yace su Janar Abdussalami sun san da mutuwar tsohon dan takarar shugaban kasa MKO Abiola wanda yace akwai abin da ya kashe sa kuma Janar Abdussalami kadai zai iya bayani.

Hakanan kuma Janar din mai ritaya yace ba shakka akwai hannun su Janar Obasanjo wajen kifar da Gwamnatin Janar Sani Abacha wanda daga karshe Marigayi Janar Abacha ya sa aka daure su bayan bincike.

KU KARANTA: Tsohon Hafsun Soji ya fasa kwai

Yadda aka hada baki da Obasanjo domin a ga bayan Abacha Inji tsohon Janar
Abdussalam ya san abin da ya kashe Abiola Inji Janar Bamaiyi

Bamaiyi yake cewa an yi yunkurin kashe shugaba Abacha ta hannun mataimakin sa Janar Oladipo Diya wanda yace bai da tantama game da wannan. Janar Bamaiyi dai yayi wadannan bayanai ne kwanan nan kamar yadda Legit.ng ke samun labari inda ya wanke Janar Abacha.

Kwanan nan kuma wani Dan Majalisar Wakilai yayi kira da shugaba Buhari ya ajiye mulki a dalilin rashin lafiya, ya kamata shugaba Buhari ya mikawa Mataimakin sa mulkin sannan ya nemi wani ya nada a matsayin mataimakin shugaban kasar daga Arewa Inji sa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani mutumi ya tsinewa Gwamnatin Najeria

Asali: Legit.ng

Online view pixel