An yi kira shugaba Buhari yayi murabus; Fadar shugaban kasa tayi bakkam

An yi kira shugaba Buhari yayi murabus; Fadar shugaban kasa tayi bakkam

Wani Dan Majalisar Wakilai yayi kira da shugaba Buhari ya ajiye mulki a dalilin rashin lafiya, sai dai har yanzu shugaban kasar bai ce komai ba game da batun

Fadar shugaban kasa tayi bakkam

Dan Majalisa yayi kira shugaba Buhari yayi murabus

Honarabul Abdulmumin Jibrin yayi kira da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ajiye mulkin kasar ya kula da sha’anin rashin lafiyar sa, Honarabul Jibrin ya bayyana haka ne a karshen makon nan ta shafin Twitter.

Sai dai har yanzu Fadar shugaban kasa ba ta maida wani martani ko jawabi ga kiran da wannan Dan Majalisa da aka dakatar yayi ba. Kamar yadda NAIJ.com ke samun labari har yanzu shugaban kasar bai tankawa wannan magana ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi sababbin nadi

An yi kira shugaba Buhari yayi murabus; Fadar shugaban kasa tayi bakkam

Dan Majalisa yace shugaba Buhari ya ajiye mulki

Honarabul Jibrin yake cewa kawai ya kamata shugaba Buhari ya mikawa Mataimakin sa mulkin sannan ya nemi wani ya nada a matsayin mataimakin shugaban kasar daga Arewa. Sai dai hakan ya jawo babban ce-ce-ku-ce a fadin kasar inda wasu ke ganin gaskiya ne da masu akasin haka.

Mai magana da bakin shugaban kasar Femi Adesina ya fadawa ‘yan jarida a jiya cewa ba zai ce komai ba tukun game da batun na aka nemi a ji ta bakin shugaban kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko an yi da-na-sanin zaben Muhammadu Buhari shugaba [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel