Kungiyar Boko Haram ta saki sabuwar bidiyo

Kungiyar Boko Haram ta saki sabuwar bidiyo

Game da cewan rahotanni, kungiyar yan tada kayar bayan Boko Haram ta saki wata sabuwar bidiyo inda take yiwa shugaban kasan Kamaru isgilanci

Kungiyar Boko Haram ta saki sabuwar bidiyo

Yan Boko Haram

Wannan shine bidiyo na biyu tun 13 ga watan Maris 2017, lokacin da yan ta’addan suka saki bidiyo cikin yaren larabci da Hausa, wanda ke nuna manyan malamai, ma’aikatun gwamnati, shugabannin dunya wanda ya kunshi Muhammadu Buhari, Donald Trump, Barack Obama da wasu shugabannin Turai.

KU KARANTA: Kungiyar matasan arewa tayi gargadi ga Yarbawa

Game da cewar Sahara Reporters, har yanzu ba’a sanya bidiyon a yana gizo ba.

A bangare guda, kakakin hukumar sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya bayyana cewa a ranan Talata, 28 ga watan Maris,misalin karfe 10 na safe, rundunar sojin 158 Task Force Battalion ta damke wasu yan leken asirin Boko Haram kwaya 2 suna leke a Kareto da Dangatti.

Bincike ya nuna cewa suna liken asirin ne domin shirin kai farmaki kauyukan guda 2.

https://twitter.com/naijcomhausa

https://www.facebook.com/naijcomhausa/#

Ga wata bidiyon da NAIJ.com ya shirya muku akan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel